Rashin Godiyar Allah: Uwa Ta Kwace Motar Da Ta Ba Diyarta Mai Shekaru 16 Kyauta a Bidiyo

Rashin Godiyar Allah: Uwa Ta Kwace Motar Da Ta Ba Diyarta Mai Shekaru 16 Kyauta a Bidiyo

  • Wata uwa ta kwace dankareriyar mota kirar Marsandi da ta siyawa diyarta a matsayin kyauta a ranar cikarta shekaru 16 a duniya
  • A wani bidiyo da ya yadu, matar ta yiwa diyar tata kyautar bazata ta mota kirar Tesla amma ga mamakinta yarinyar ta yi watsi da motar cewa Marsandi mai kalar ruwan hoda take so
  • Bayan ta dauke idanu daga martanin jama'a, matar ta sauya motar Tesla din zuwa Benz amma kuma yanzu ta janye kyautar

Yan kwanaki bayan ta siyawa diyarta mai shekaru 16 motar Marsandi, wata uwa ta kwace abun ta domin koyawa yarinyar hankali kan rashin da'a da a nuna.

Ku tuna cewa a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, matar ta siyawa diyar tata mota kirar Tesla fara a ranar zagayowar ran haihuwarta amma sai yarinyar ta yi watsi da kyautar ba tare da ta nuna godiya ba.

Kara karanta wannan

Za Ki Dandana Kudarki: Yadda Wata Uwa Ta Tsinewa Diyarta Da Ta Yi Aure Ba Tare Da Saninta Ba

Mace, mota da wayoyi
Rashin Godiyar Allah: Uwa Ta Kwace Motar Da Ta Ba Diyarta Mai Shekaru 16 Kyauta a Bidiyo Hoto: @neshieslife2340
Asali: TikTok

Yayin da take watsi da motar, matashiyar ta fada ma mahaifiyar tata cewa ita Marsandi launin ruwan hoda take so. Matar ta je ta siyawa yarinyar Marsandi din, kamar yadda ya bayyana a bidiyon da ta wallafa a TikTok.

Sai dai kuma, a yanzu uwar ta janye kyautar da ta yi mata ta hanyar kwace motar. A sabon bidiyon da ta yi, ta bayyana cewa lallai diyarta ta nuna rashin da'a kuma akwai bukatar a koya mata darasi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matar ta kwace komai na diyar tata

Da take baje kolin kayayyakin a kasa, matar ta ce baya ga motar da ta karba, ta kwace mayar hannu, jaka da wayar ipad din yarinyar.

Ta ce mijinta ya karbe makullin motar. Matar ta ce shawara ce da suka yanke tare ita da mijinta. Kalamanta:

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Ta yi aure a shekaru 50, ta haihu a shekara 71, bidiyon tsohuwa ya ba da mamaki

"Na tattauna da mahaifinta kuma mun yanke shawarar cewa za mu kwace komai nata har sai ta sauya halinta. Mahaifinta ya karbi makullin motar kuma yana so ya siya ma yarinyar keke saboda ta nuna rashin da'a.
"Bugu da kari, ku masu cewa ni ba uwa ta gari bace, ni uwa ta gari ce. Uhmmm, ina kaunar yarana kuma ina kokarin mallaka masu duk abun da suke so, wasu ma wanda ni ban samu ba da nake yarinya.
"Amma kun yi gaskiya idan aka zo batun rashin da'a. Yau ce ranar karshe a bangarena don haka na kwace komai kuma yanzu tana zaune a dakinta ba tare da komai ba."

Da take korafi kan rashin da'ar diyar tata a bidiyon da ya yadu, matar ta ce yarinyar ta kan yi godiya kuma wannan ne dalilin da yasa ta ke siya mata komai take so, don haka ta cika da mamaki.

Kara karanta wannan

Ma'aikaciyar da ke Zuwa Aiki a Kasa Kullum ta Tsinta N6.908m, Ta Kai Cigiya An Samu Masu Kudin

Kari a kan horar da diyar tata na watanni uku, matar ta bukace ta da ta rubuto wasikar ban hakuri.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

T O N I ta ce:

"Babu laifi a cikin baiwa danka abun da kai baka samu ba amma duk da haka ba za ka kawo mun rashin tarbiya ba."

user5004054001746 ya ce:

"Bata cancanci mota ba. Ke da mijinki kun yi aiki tukuru don tara kudinku tunda ta nuna rashin godiya ku sa ta tafiya da kafarta."

Budurwa ta shiga dimuwa, tana ta ihun neman ceto daga yan boye

A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan ganin bidiyon wata matashiya da ke rusa kuka da ihu cewa a kawo mata agaji domin dai wasu mutanen boye na bibiyar rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel