An Tsare Dan da Ga Gwamna Yahaya Bello Bisa Laifin Damfara Ta N3bn a Gidan Yari, Ana Neman Matar Gwamna

An Tsare Dan da Ga Gwamna Yahaya Bello Bisa Laifin Damfara Ta N3bn a Gidan Yari, Ana Neman Matar Gwamna

  • Wata kotun tarayya ta mika dan uwan gwamnan APC a jihar Kogi zuwa gidan yari bisa zargin badakalar kudade masu yawan gaske
  • EFCC ta gurfanar da Ali Bello ne a gaban kotu tare da wasu mutanen da ake zargin sun hada kai sun saci kudaden da suka kai N3bn
  • Za a ci gaba da sauraran kara a ranar 13 ga watan Faburairu don sake jin tushen kudin da kuma hujjojin EFCC

FCT, Abuja - A ranar Laraba 8 ga watan Faburairu ne hukumar EFCC ta gurfanar da dan da ga gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a gaban mai shari'a Obiora Egwuatu na kotun tarayya da ke Abuja.

An gurfanar da Ali Bello ne kare da Abba Adauda, Yakubu Siyaka Adabenege, Iyada Sadat da Rashida Bello da ake nema bisa zargin aikata laifuka 18 na sama da fadin N3,081,804,654.00.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kasa ta birkice, 'yan Najeriya sun fara zanga a hedkwatar CBN bayan hukuncin kotu

A cewar rahoton Tribune Online, Rashida Bello ce matar gwamnan jihar Kogi, kuma ana nemanta don amsa wannan tuhuma na EFCC.

Kakakin hukumar EFCC, Wilsom Uwujaren ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Punch ta ruwaito.

Matar gwamna da dan uwanta sun saci kudi
An Tsare Dan da Ga Gwamna Yahaya Bello Bisa Laifin Damfara Ta N3bn a Gidan Yari | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan karanto musu laifukansu, sun musanta zargin da ake musu ga dukkan laifukan 18 da aka ambata.

An tasa keyar Ali Bello zuwa magarkama

Duba da wannan, lauya mai gabatar da kara, Rotimi Oyedepo, SAN a nemi kotu ta da ranar da za a yi shari'a domin ba EFCC gabatar da hujjojinta.

Sai dai, lauyan wadanda ake kara, Ahmed Raji, SAN ya nemu kotun da ta ba da belin wadanda yake karewa ya zuwa lokacin da za a sake sauraran karan, rahoton PM News Nigeria.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari na ganawar sirri da gwamnan CBN bayan hukuncin kotun koli kan batun kudi

Mai shari'a ya dage karar zuwa 13 ga watan Faburairun 2023, tare da ba da umarnin a tsare wadanda ake zargin a gidan yari har sai sun cancanci beli.

Ba wannan ne karon farko da ake daure wani na kusa da gwamna ko wani dan siyasa ba a Najeriya bisa zargin sace kudi.

A shekarar da ta gabata ne aka tabbatar da hukuncin dauri kan dan tsohon shugaban hukumar fansho, Faisal Abdulrasheed Maina bisa laifin hada hannu da mahaifinsa wajen sace kudin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.