Buhari Ya Yi Nadin Wasu Mukamai 10 a Rana Daya a Jihohin Kano, Abia da Delta

Buhari Ya Yi Nadin Wasu Mukamai 10 a Rana Daya a Jihohin Kano, Abia da Delta

Ma’aikatar ilmi ta ce Muhammadu Buhari ya amince da wasu nade-naden mukamai da aka yi

Mai girma Shugaba Najeriya ya yarda da nadin sababbin shugabanni a makarantun koyon aiki

Sanarwar tace nadin mukaman ya shafi wasu makarantu a garuruwan Orogun, Kabo da Isuochi

Abuja – Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin shugabanni da manyan jagorori a wasu makarantun gaba da sakandare da ke kasar nan.

Punch ta ce sanarwa ta fito daga ma’aikatar ilmi cewa an nada sababbin shugabanni a makarantun tarayya na koyon aiki da ke Abia, Kano da Delta.

Dr. Paul-Darlington Ndubuisi ya zama shugaban makarantar koyon aiki na garin Isuochi a Abia, Dr. Duke Okoro zai rike makarantar da ke Orogun.

Ma’ikatar ilmi ta tabbatar da Farfesa Mohammed Magaji a matsayin shugaban irin wannan makaranta ta tarayya da ke garin Kabo a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wadanda aka nada za su sauka a 2028

A jawabin da aka fitar, kowanensu zai yi shekaru biyar a ofis daga ranar 17 ga watan Junairu 2023, wa’adi guda kurum suke da shi, babu damar tazarce.

Darektan yada labarai da hulda da jama’a na ma’ikatar tarayyar, Ben Goong ya ce an amince da nadin sababbin magatakardu na makarantun nan uku.

Buhari
Buhari a zaman FEC Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

An kawo sababbin magatakardu

Wadanda aka zaba a matsayin magatakardu a makarantun na Abia, Kano da Delta su ne: Christine Aluyi, Umar Dumbulum da kuma Ezenuruihe Olachi

A sanarwar ne kuma aka fahimci Atabatele Solomon da Nkpado Pamela sun zama ma’aji a makarantun koyon aiki da ke garuruwan Kabo da Orogun.

Tribune ta ce a karshe an amince da Dr. Iroroeavwo Edwin Achugbue da Kabiru Ubale a matsayin masu kula dakunan karatu a makarantun Delta da Kano.

Kara karanta wannan

Katobarar Tinubu: Gaskiya ta fito, Naja'atu ta fadi ainihin dalilin da yasa Tinubu ke kwafsawa

Shugaba, magatakarda, ma’aji da kuma babban jami’in kula da dakunan karatu su ne manyan masu kula da manyan makarantun da ke gaba da sakandare.

Malam mai aikin assha

Kun ji labari ana rade-radin wani Malami a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ya dankarawa dalibarsa ciki, daga baya kuma suka yi aurensu.

Zargin da ake yi shi ne matar ce ta ke kawowa mijinta dalibai har gida da nufin ayi aikin assha. Hukumar Hisbah ta samu labari, kuma ta na yin bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng