Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Rasa Kawunsa Ana Gab da Zabe

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Rasa Kawunsa Ana Gab da Zabe

  • Ana shirin babban zaben shugaban ƙasa a wannan watan, Goodluck Jonathan ya rasa kanin mahaifiyarsa mai shekaru 87
  • Omieworio Afeni ya rasu ne a karshen makon nan a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Tsohon shugaban ya bayyana mamacin da Dattijo mai hikima kuma iyalansa na cikin radaɗi mai ciwo sakamakon wannan rashi

Bayelsa - Tsohon shugaban ƙasa a Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya rasa kawunsa, Omieworio Afeni. Mamacin ya rasu ne yana da shekaru 87 a duniya.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Mista Afeni ya mutu ne a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a karshen makon nan bayan yar gajeruwar rashin lafiya.

Dakta Goodluck Jonathan.
Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Raba Kawunsa Ana Gab da Zabe Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Mamacin ya kasance ƙanin mahaifiyar tsohon shugaban Jonathan. Rahoto ya nuna cewa tun bayan rasuwar kawunsa, Goodluck Jonathan, bai bar jihar Bayelsa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zanga-Zanga Ya Barke a Abeokuta kan karancin Naira da tsadar mai, an kai hari Banki

Bayanai sun nuna cewa Jonathan tare da mahaifiyarsa da sauran iyalan gidansu na ci gaba da karban gaisuwa da masu jaje tun da aka tabbatar da rasuwar Mista Afeni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata sanarwa da ofishin watsa labarai na Jonathan ya fitar, an ji tsohon shugaban ƙasan na cewa iyalan gidansu na cikin matsanancin radadin wannan rashi.

Jonathan ya bayyana cewa, "Iyalan mu na cikin radaɗi mai ciwo na wannan rashi amma mun gode Allah bisa ni'imar doguwar rayuwa mai cike da tarin nasarori."

Haka zalika ya ayyana mamacin da mutumin da ba kasafai ake samun irinsu ba wanda ya kai gwauro ya kai mari wajen gina zaman lafiya da haɗin kai a yankinsu.

Mista Jonathan ya kara da jaddada cewa babu tantama, "Zasu yi kewar dattijo Omieworio Afeni saboda hikimarsa da kuma wayewar shawarinsa masu amfani."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IPMAN Ta Umurci Mambobinta Su Rufe Dukkan Gidajen Mai A Borno

Yaushe za'a yi bikin birne mamacin?

Bayanai sun nuna cewa za'a yi bikin birne mamacin a ranar 23 ga watan Maris, 2023 amma sauran shirye-shiryen bikin zasu fito daga iyalan gidan marigayin nan gaba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma Wani Basaraken gargajiya mai ƙima.ya kunyata yayin da ya je neman cire sabbin takarsun kuɗi a Banki

Daga zuwansa, Jama'a suka buɗa masa hanya ya wuce kai tsaye kasancewarsa Uba kuma Basaraken da suke martabawa amma duk da haka ma'aikatan bankin suka ƙi saurarensa.

Bayan wasu mintuna Basaraken ya koma cikin mota ya bar wurin kuma daga baya dandazon mutane suka kutsa kai ta tsiya cikin bankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262