“N1,000 Na Biya Kan Kowace Litar Mai Daya”: Oshiomhole Ya Koka a Bidiyo
- Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya koka kan siyan litar man fetur a N1,000
- Oshiomhole ya koka cewa duk da kashe fiye da naira tiriliyan kan tallafin mai, yan Najeriya na biyan fiye da farashin kasuwa
- A cewar Oshiomhole, N7trn kan tallafin mai bai kunshi kudaden ci gaban fetur ba, yana mai cewa dole a rike wani kan haka
Adams Oshiomhole, tsohon shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya koka kan tsadar farashin man fetur a Najeriya.
Da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels TV, tsohon gwamnan na jihar Edo, ya koka cewa ya siya litar mai kan N1,000.
Akwai mai hannu a karancin man fetur Oshiomhole
Oshiomhole ya ce lamarin ba abun dariya bane, yana mai cewa wani na da hannu a karancin man fetur a kasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce a yanzu haka, kasar na kashe kimanin naira tiriliyan 7 kan tallafin man fetur amma abun takaici shine cewa yawancin yan Najeriya na biyan fiye da farashin da ya kamata a siyar da mai a kasuwa.
Tsohon Shugaban kungiyar kwadago na kasar ya bayyana cewa duk da naira tiriliyan 7 na tallafin mai, akwai kuma wani kudin haraji na fetur, yana mai jaddada matsayinsa na farko cewa wasu ne ke da hannu a lamarin.
A cewarsa, idan yan Najeriya suna ganin ba sabon abu bane cewa mun saba samun karancin man fetur hatta a mulkin soja har zuwa Shugaba Olusegun Obasanjo, Yar’adua da Jonathan, ana iya cewa karancin mai ya zama dadaddiyar matsala amma wannan baya nufin abun yarda ne.
Tun a Janairu 2022 me kasar ke fama da matsalar karancin man fetur da tsadar farashi a yankuna daban-daban na kasar.
Karancin Man fetur da kudi: Rai daya ya salwanta yayin da rikici ya kaure tsakanin jami'an tsaro da yan daba
A wani labari na daban, zanga-zanga kan karancin man fetur da takardun kudi ya zama rikici a garin Ibadan da ke jihar Oyo.
Fada ya kaure tsakanin jami'an tsaro da yan daba lamarin da ya yi sanadiyar rasa ran wani dan sa-kai.
Asali: Legit.ng