Wata Mata ’Yar Najeriya Ta Kayatar, Ta Yi Aure Tana da Shekara 50 Ta Haihu Tana da Shekara 71 a Duniya
- Wata mata mai yawan shekaru da ta cire tsammanin haihuwa ta zama uwa bayan ta kai shekeru 71 a duniya
- Matar ta shiga farin ciki yayin da take nuna lafiyayyiyar jaririyarta, inda tace ta haihu cikin sauki a kasa da mintuna 10
- Wata ‘yar uwar mai jegon ce ta sanya ta yin aure a lokacin tana da shekaru 50, kuma sai da ta jira shekaru 21 kafin ta samu karuwa
Wata mata ‘yar Najeriya mai shekaru 71 ta shiga farin ciki da annashuwa bayan da Allah ya azurta ta da haihuwa bayan shekaru 21 da aurenta.
Uzo Oge, wata ‘yar uwar mai jegon ta ziyarce ta a Fatakwal tare da mahaifiyarta domin nuna farin cikinsu da yin barka ga samun wannan karuwa.
Da take daukar abin da ya faru a daudaukar kamera, Oge ta yada bidiyo a TikTok tare da cewa, mai jegon ta yi aure ne a lokacin tana da shekaru 50 kuma har ma ta cire tsammanin haihuwa.
A bidiyon, an ga lokacin da take murna, take godewa Allah bisa ba ta kyautar jaririyar da bata yi tsammanin samu ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A bangaren ‘yar uwar Oge, ita ma ta nuna farin ciki da wannan kyauta. Daga nan mai jegon ta dauke su zuwa cikin gida tare da nuna musu lafiyayyiyar jaririyarta.
A cewar mai jegon, bai dauke ta minti 10 ba lokacin da take nakuda ta haifi jaririyar cikin sauki ba tare da wata wahala ba.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a
Jama’a a kafar sada zumunta sun ce ba za a yi babu su ba, sun shiga sahun taya murna da kuma addu’ar Allah ya raya. Ga kadan daga maganganunsu:
WONDER:
"Ina mahaifin yake, na matukar damu na sanin lafiyar mijin.”
"Ina taya ki murna.”
@chiichii<3:
A Baya Ba na Kula Yara: Budurwar da ta Auri Wanda ta Girma Tace Tana Cikin Farin Ciki, Har Sun Haihu
"Chaii wannan lamari ya saka ni kwalla! Babu abin da Allah ba zai iya ba, abin al’ajabi.”
Eli Tan:
"Ina taya ki godiya ga Allah tare da murna mama. Dama Allah bai bukatar umarni wajen ba da albarkarsa gareki.
adviser:
“Ki godewa Allah mama za ki rayu ki kula da jaririyar, dukkan uwaye za su rayu su kula da jariransu da yardar Allah.”
Virtue Michael:
“Babu abin da Allah ba zai iya ba, ina gode masa kuma na tabbatar zai cika min buri, na yi imani dashi.”
Allah ne mai ba da kyautar haihuwa, kwanaki wani tsoho mai shekaru 83 ya samu arzikin jariri.
Asali: Legit.ng