Budurwar da Tace ba Zata Auri wanda ta Girma ba, Ta Auri Yaro Har Sun Haihu

Budurwar da Tace ba Zata Auri wanda ta Girma ba, Ta Auri Yaro Har Sun Haihu

  • Wata mata daga bisani ta auri wani matashi da ta girma da shekaru biyu bayan ta gama kurin ba za ta auri yaro ba
  • Shekaru biyar da aurensu tare da haifar 'ya'ya, bidiyon da ta wallafa ya nuna yadda suke zaman lafiya da juna tare da farin ciki
  • Mata da dama sun yo ca a kanta a sashin tsokaci gami da labarta yadda suka girmi mazajensu kuma suke zaune lafiya da su

Wata mata, @chenayxo26, wacce ta ce bata taba soyayya da yaro ba lokacin tana da shekaru 25 kacal ta canza ra'ayinta gami da yin wuff da wani matashi da ta girma.

Matar aure
Budurwar da Tace ba Zata Auri wanda ta Girma ba, Ta Auri Yaro Har Sun Haihu. Hoto daga @chenayxo26
Asali: TikTok

Wani bidiyo da ta wallafa ya nuna lokacin da ta auri wani matashi mai shekaru 23, wanda suke zaune lami lafiya da 'ya'yansu. Mata da dama sun bayyana yadda suka girmi mazajensu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yaro Dalibin Najeriya Yana Shan Garin Kwaki Cikin Dalibai 'Yan Uwansa, Tamkar Yana Cin Shinkafa

Ta kara da cewa, shekaru biyar kenan da aurensu, tana zaune cikin farin ciki bata taba barin tazarar shekarun da ke tsakaninsu ya hana ta farin ciki ba.

Yayin da matar ta ce shekaru ba su ne hankali ba, mutane da dama a sashin tsokacin sun yarda da batunta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya janyo sama da tsokaci 100 da sama da jinjina 30,000.

Martanin jama'a

Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a:

Sarah Bee ta ce:

"Namiji, nima na fadi irin haka. Ubangiji ya yi magani na da wuri, abun dariya."

Kimberly Osei1132 ya ce:

"Mazan da suka girme ka har barazana suke maka."

swechchha bhattarai ta ce:

"Ni da na gano na girmi miji na da shekaru hudu."

Hannah Brinson810 ta ce:

Kara karanta wannan

Soyayya Gamon Jini: Dirarriyar Matar Aure ta Bayyana Wadan Mijinta a Bidiyo, Tace Suna Cikin Farin Ciki

"Nima na girmi miji na."

MrsLets4 ta ce:

"Na dade ina fadin haka tsawon rayuwata, wannan karon fa Ubangiji ya yi magani na, na ba miji na shekaru biyar.. Shekarar mu hudu da aure, yanzu haka ina da juna biyun shi na uku."

Frekuma ta ce:

"Ban damu da tazarar shekarun ba kwata-kwata. In dai mutum na da hankali da tunani kuma muna son juna."

Attajitri mai taimakon al'umma ya haukace, ya koma rawa a kasuwa

A wani labari na daban, wani attajiri da ya saba taimakon al'umma ya haukace inda yake kwasar rawa a cikin kasuwa.

Wani ma'abocin amfani da TikTok ya sanar da irin taimakon al'umma da ya ke yi amma yanzu babu wanda ya kai masa dauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel