Ya Kamata a ’Yan Najeriya Su Yiwa Shugaba Buhari da Gwamnan CBN Emefiele Uzuri, Inji Peter Obi
- Dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ba CBN uzuri kan batun sauyin kudi
- Hakazalika, ya yi kira ga CBN da ya saukake hanyoyin samun sabbin kudade a Najeriya don rage wahala
- Atiku Abubakar a baya ya ce kada a kara wa'adin amfani da tsoffin kudade saboda dalilai na siyasa
Najeriya - Yayin da ake ta’allaka laifin karancin sabbin Naira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan CBN Godwin Emefiele, Peter Obi ya ce hanzari ba gudu ba.
Dan takarar shugaban kasan a jam’iyyar Labour ya bayyana cewa, akwai bukatar a yiwa Buhari da Emefiele uzuri game da wannan sauyi na wucin gadi.
Obi ya yi wannan kira ne ga ‘yan Najeriya ta shafinsa na Twitter a ranar Lahadi 5 Faburairu, 2023.
Sauyi ne mai kyau, inji Obi
A cewarsa, ba wannan ne karon farko da aka fara sauya kudi ba a duniya, kasashe da yawa sun yi hakan, kuma an taba yi a Najeriya ma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma shaida cewa, wannan sauyi duk da yana da wahalar da yake tattare dashi, amma tabbas zai amfani kasar ta hanyoyi da yawa na tsawon lokaci.
A cewarsa:
““Ina rokon ’yan Najeriya da su yi wa CBN da gwamnatin tarayya uzuri kuma su yi fatan al’umma da kasa baki daya za su ci gajiyar sauyin da aka yi."
Ya kamata CBN ta yawaita adadin sabbin Naira
A bangare guda, ya yi kira ga CBN da sauran bankunan kasuwanci da su daura damarar kara adadin sabbin kudaden da ke yawo a hannun jama’a.
Ya kuma yi kira ga samar da asusun banki ga wadanda basu dashi a kasar domin saukake hada-hadar kasuwanci da rayuwar yau da kullum a kasar.
Karancin Naira: Wike Ya Aike Wa Buhari Sako A Fakaice, Ya Ce, "Ina Son Ka Gama Lafiya", Kalli Bidiyon
A fahimtar Obi, hakan ne zai rage wahalan da ‘yan Najeriya ‘yan uwansa ke ciki, musammam ma talakawa da ke kauyuka da yankunan karkara.
Atiku ya ce kada a daga wa'adin daina amfani da tsoffin kudi
Ba Obi ne ya fara wannan batu ga gwamnati ba, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya yi irin wannan kira, inda yace kada a kara wa’adin da aka dauka na daina amfani da tsoffin kudade.
Idan baku manta ba, an yi sabbin kudi N200, N500 da N1000 a Najeriya, kuma za a daina amfani da tsoffi a ranar 10 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Asali: Legit.ng