Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Gillar Da Yan Bindiga Suka Yi Wa Yan Sa-Kai a Katsina
- Shugaban kasa Buhari ya yi martani a kan mummunan harin da yan bindiga suka kaiwa yan sa-kai a jiharsa ta Katsina
- Yan bindiga sun kai harin kwauton bauna kan yan sa-kai a yayin da suka bi sahunsu don kwato shanu da dabbobin da suka sace
- Da yake mika ta'aziyyarsa ga yan uwan mamatan, Buhari ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwarsu ga garuruwansu ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da mummunan harin da yan bindiga suka kai wa yan sa-kai a dajin Yargoje da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Wasu yan bindiga sun kai harin kautan bauna kan ayarin yan sa-kai a dajein yayin da suka je kwato dabbobin da maharan suka sace, lamarin da ya kai ga kisan, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Karancin Mai Da Kudi: An Yi Kare Jini Biri Jini Yayin Zanga-zanga a Wata Jahar Najeriya, An Kashe Mutum Daya
Ba za a manta sadaukarwar wadannan jarumai ba, Buhari
Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya saki a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, ya yi ta'aziyya ga dukkanin yan sa-kai da yan uwan wadanda suka mutu a harin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaba Buhari ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwar jaruman mazan ba wadanda ke aiki ba ji ba gani don hana aikata laifuka da hukunta masu yinsa a garuruwansu, rahoton The Nation.
Buhari ya yi wa mamatan addu'a inda ya ce:
"Tunaninmu da addu'o'inmu na tare da yan uwan mamatan a wannan mawuyacin lokaci. Allah ya ji kan wadanda suka rasun."
Harin kwauton bauna: Yan ta'adda sun kashe yan sa-kai a dajin Katsina
A baya mun ji cewa an yi arangama tsakanin yan ta'adda da kungiyar tsaro ta yan sa-kai a jihar Katsina lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla guda 41.
Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar al'amarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.
Isah ya ce yan sa-kai daga kauyuka 11 a karamar hukumar Bakori, sun hadu sun bi sahun yan maharan da nufin karbo shanu da suka sace. Sun gano su a wani wuri a dajin Yargoje inda yan ta'addan suka musu harin kwaton bauna.
Karancin Naira: Fada ya kaure tsakanin masu zanga-zanga da jami'an yan sanda a Ibadan
A wani labari na daban, mun ji cewa rikici ya kaure yayin da mazauna a jihar Oyo suka gudanar da zanga-zanga kan karancin Naira da man fetur.
An yi arangama tsakanin jami'an tsaro da wasu yan daba lamarin da ya yi sanadiyar rasa ran wani mutum daya.
Asali: Legit.ng