ICPC Ta Bankado Sabbin Naira Da Aka Boye a Durowan Banki, Ta Saki Bidiyo

ICPC Ta Bankado Sabbin Naira Da Aka Boye a Durowan Banki, Ta Saki Bidiyo

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta sake bayyana cewa bankuna na da hannu a karancin sabbin takardun kudi da ake fama da shi a kasar
  • ICPC ta saki wani bidiyo na daya daga cikin ayyukanta inda aka bankado sabbin kudi boye a wani durowa
  • Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon yayin da CBN ta hada kai da ICPC da sauran hukumomin kudi da tsaro don magance karancin sabbin kudi a kasar

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gano damin sabbin kudi da aka boye a cikin durowan wani banki.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 4 ga watan Fabrairun 2023 don jama'a su gani, an gano jami'an hukumar suna umurtan wani banki da ya bude durowan ajiyar kudinsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yaro Dalibin Najeriya Yana Shan Garin Kwaki Cikin Dalibai 'Yan Uwansa, Tamkar Yana Cin Shinkafa

Sabbin naira
ICPC Ta Bankado Sabbin Naira Da Aka Boye a Akwatunan Banki, Ta Saki Bidiyo Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Da aka bude durowan, jami'in bankin ya dage yana mai nuna cewa babu sabbin kudi a ciki.

Sai dai kuma, jami'an ICPC basu yarda ba sannan suka dage cewa jami'an su firfito da kayan cikin durowan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bayan tsoffin takardun kudin yan N1,000, sai ga tarin sabbin kudi da aka boye a kasa-kasan durowan.

ICPC ta dauki karin alkawari

A halin da ake ciki, hukumar ICPC ta yi alkawarin bi ta kan mutanen da ke wahalar da kokarin da ake yi na ganin sabbin kudin sun isa ga jama'a.

Tuni aka kama jami'an wasu bankuna kan zargin yi wa tsarin zagon kasa kuma ana sanya ran za a kama wasu a kwanaki masu zuwa.

Jama'a sun yi martani

@FoucaultzWizdom ya rubuta:

"Na jinjinawa wannan aiki na ICPC kuma na yaba da kokarinsu. Abu mafi ciwo shine gane cewa hukumomin Najeriya za su iya yin aikinsu idan har suka so."

Kara karanta wannan

Karshen alewa: An kama manajan bankin da ke boye sabbin kudi yana hana 'yan Najeriya

@DonPatrawa ya rubuta:

"Ku ji fa yadda suka boye kudi suna ajiyarsu ga yan siyasa da yan ta'adda. Ya kamata a rufe irin wadannan bankunan."

@AbooBilaaal ya yi martani:

"Dan Allah ICPC ku zo Asaba za ku ga karin irin wadannan bankuna da dama."

Gwamnatin Kaduna ta umurci asibitoci su dunga karbar 'transfer'

A wani labarin, hukumar tattara kudaden haraji ta jihar Kaduna ta umurci asibitocin gwamnati da su fara karbar 'transfer' yayin hada-hadar kudi.

Hukumar KADIRS ta ba da wannan umurnin ne domin saukakawa jama'a a wannan yanayi na ake ciki na karancin kudade a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng