Kungiyar Lauyoyi Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan ’Yan Bindiga Sun Kashe Alkali Yana Tsaka da Yanke Hukunci
- Kungiyar lauyoyi ta Najeriya ta yi Allah-wadai da kisan da aka yiwa wani alkali yana tsaka da yanke hukunci
- A ranar Juma'a ne aka samu labarin yadda wasu 'yan bindiga suka kutsa cikin kotu, suka sheke wani alkali
- Kungiyar NBA ta nemi gwamnati ta gaggauta daukar mataki don kiyaye faruwar hakan a nan gaba
Jihar Imo - Kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta fusata, ta bayyana bacin ranta da yadda aka kashe wani alkali lokacin da yake yanke hukunci a kotu a jihar Imo.
Kungiyar ta yi Allah-wadai da yadda ‘yan bindiga suka hallaka mai shari'a Nnaemeka Ugboma a karamar hukumar Oguta a jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, BBC ta ruwaito.
Bacin ran kungiyar na fitowa ne daga cikin wata sanarwar da sakataren yada labaranta Akorede Habeeb Lawal ya fitar, inda ya tabbatar da kisan alkalin a ranar Juma’a 3 ga watan Janairun 2023.
Wasu wadanda suka ga lokacin da aka yi kisan sun ce, an harbe alkalin ne bayan da ya kammala yanke wani hukunci kan wata shari’a da ke gabansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kwace wayoyin jama'a, an kashe alkali
A cewarsu, an ga isowar ‘yan bindigan ne da yawansu, kuma da zuwansu kotun suka karbi wayoyin kowa da ke ciki kana suka bindige alkalin.
Kungiyar ta ce kisan Ugboma babban abin damuwa ne, kuma kisan ma’aikatan shari’a na kokarin zama ruwan dare a Najeriya.
A bangare guda, ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar mataki tare da kare ‘yan Najeriya a duk inda suke, The Nigerian Lawyer ta ruwaito.
Hakazalika, ta nemi a tura jami’an tsaro a harabar duk wani kotu a jihar Imo don tabbatar da ba a sake cutar da wani ma’aikacin shari’a ba a yankin.
Ya zuwa yanzu NBA na ci gaba da bincike don gano makasan alkalin tare da tabbatar da an gurfanar dasu a gaban kuliya manta sabo.
Rahotonmu na baya ya bayyana yadda 'yan bindigan suka kutsa har cikin kotu suka hallaka wannan alkali.
Ya zuwa yanzu dai ba a gano musabbabin shiga wannan kotu ba, kana ba a gano wadanda suka yi barnar ba.
Asali: Legit.ng