An Gano Gawar Mata Da Yaran Basaraken Arewa Da Yan Bindiga Suka Sace Cikin Mummunan Yanayi
- Sarkin garin Mutumbiyu a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba ya ce an gano gawar iyalansa
- Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace matansa biyu da yaransa biyar kimanin kwana 14 da suka wuce
- Daga bisani daya cikin yayansa ya tsere daga sansanin yan bindigan an dawo da shi gida sai dai sauran iyalan dukkansu a mace aka tsinto su
Jihar Taraba - Basaraken Mutumbiyu da ke jihar Taraba, Mai shari'a Sani Muhammad (mai murabus) ya ce an gano gawar matansa biyu da yaransa biyar, rahoton The Punch.
Sarkin ya fada wa wakilin Daily Trust a hirar wayar tarho cewa an gano gawarwarkin ne a safiyar ranar Asabar, 4 ga watan Fabrairun 2023 har sun fara lalace wa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce za a birne su a garin Mutumbiyu.
Kalamansa:
"An gano gawar iyalai na da masu garkuwa da mutane suka kashe kuma za a kawo su Mutumbiyu."
Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace iyalan basaraken a gidansa da ke Jalingo kimanin makonni biyu.
Amma yaro dan shekara 14 cikin iyalan basaraken da aka sace ya tsere daga hannun masu garkuwar kwanaki biyu da suka wuce kuma an kai shi fada.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng