Karancin Sabbin Naira: "CBN Da Emefiele Sun Yi Wa Buhari Karya," Hadimin Buhari Ya Yi Zargi

Karancin Sabbin Naira: "CBN Da Emefiele Sun Yi Wa Buhari Karya," Hadimin Buhari Ya Yi Zargi

  • A yayin da yan Najeriya ke cigaba da shan wahala saboda aiwatar da tsarin canjin tsaffin naira, bisa alamu hadimin shugaban kasa baya jin dadi
  • Ajuri Ngelale, babban mataimaki na musamman ga Shugaba Buhari kan harkokin al'umma ya ce akwai matsala kan yadda aka aiwatar da tsarin
  • Ngalale ya ce babban bankin na Najeriya ta ki sanar da shugaban kasar ainihin bayani kan kallubalen da yan Najeriya ke fuskanta a yayin neman sabbin takardun nairan

Babban mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin al'umma, Ajuri Ngelale ya soki aiwatar da tsarin sauya sabbin naira da CBN ta yi karkashin jagorancin Gdowin Emefiele.

Ya kuma yi zargin cewa shugaban babban bankin na kasa, Godwin Emefiele ya ki fada wa shugaban kasa ainihin abin da ke faruwa a kasar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Bayyana 'Yan Najeriya Kwanakin da Za a Kwashe Kafin Matsalar Sabbin Kudi Tazo Karshe

Emefiele da Buhari
Karancin Naira: "CBN Da Emefiele Sun Yi Wa Buhari Karya," Hadimin Buhari Ya Yi Zargi. Hoto: Bashir Ahmed
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke magana a hirar da aka yi da shi a TVC News, Ngelale ya ce yan Najeriya na fuskantar wahala bisa tsarin sauya sabbin nairarin a kasa.

Ya ce:

"A wannan matakin, kowa na iya ganin cewa akwai matsala tattare da yadda aka aiwatar da tsarin sauya nairan.
"Mutane da dama suna cikin kunci, muna ganin mutane da dama suna kwana kusa da ATM da fatan za a saka sabbin naira a cikin ATM din.
"Muna ganin mutane a titi suna dambe a kokarin shiga banki da fatan samun sabbin nairan."

A yayin da ya ce tsarin abu ne mai kyau, ya ce aiwatarwar ba a yi shi yadda ya dace ba.

Ya kara da cewa:

"Abin da muke kokarin yi shi ne tabbatar da cewa Shugaban kasa ya samu ingantaccen bayani kuma rahoton da babban bankin Najeriya ya bayar na cewa sun samar wa dukkan bankuna a Najeriya da wadataccen adadin sabbin takardun naira karya ne.

Kara karanta wannan

Karina Bayani: Gwamnonin APC Sun Roki Buhari Ya Bari a Dinga Amfani da Tsofaffi da Sabbin Kudi

"A bayyane yake a wannan lokaci kuma ba shakka, Shugaban kasa kasancewarsa mai kaunar jama'a... ya yi abin da ya dace bisa bayanan da aka kai masa kuma yana samun bayanan karya daga Babban Bankin kuma ya tsawaita wa'adin daga 31 na Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel