Bayan Ruftawar Gini A Abuja, Minista Ya Umurci A Kamo Dukkan Masu Alhakin Kula Da Ginin
- Malam Mohammed Bello, ministan babban birnin tarayya Abuja ya umurci a kamo jami'ai kula da gine-gine a Abuja
- Umurnin na zuwa ne bayan wani gini mai bene biyu da ake aikinsa a Abuja ya rufta, ya danne mutane a kalla 24, uku sun mutu
- Ministan ya ce binciken farko da aka yi ya nuna ba a bi ka'idojin da suka dace ba yayin ginin da ma shirya filin
FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Bello, ya bawa jami'an tsaro umurnin su kama jami'an hukumar kula da gidaje na Abuja da mai kula da gini mai bene biyu da ya rufta a Abuja.
Umar Shuaibu, shugaban hukumar kula da birnin Abuja, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da ya yi da manema labarai a ranar Asabar, rahoton The Punch.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya bada umurnin a kama jami'an FHA da aka dora wa alhakin sa ido kan gine-gine, da bada izinin gini, da mai yin ginin, da injiniya da ke kula da aikin, kan zargin kisa.
Shuaibu ya bayyana cewa ginin da ake kan yinsa ya rufta kwana biyu da suka shude a 6th Avenue Gwarimpa Estate, ya danne mutane 24, an tabbatar uku cikinsu sun mutu, yayin da an ceto 21.
Ministan, yayin ziyarar da ya kai wurin, ya jinjinawa iyalan wadanda abin ya shafa da mazauna Abuja kan afkuwar lamarin, Guardian ta rahoto.
Ministan da ya samu wakilcin babban sakataren hukumar kula da birnin tarayya, FCDA, Shehu Ahmad, ya ce:
"Wannan na zuwa ne a lokacin da muke kokarin fitowa daga wannan abin damuwar na rushewan gidaje.
"Wannan ba abin da aka saba gani bane a Abuja, amma wasu wadanda ba su iya aiki ba, abin ya zo Abuja, kuma ba mu murna da hakan."
Binciken farko ya nuna an saba ka'idojin gini - FCTA
Ministan ya ce wannan shine karo na uku da irin hakan ke faruwa a Gwarimpa Estate.
Ya ce:
"Binciken farko ya nuna filin da aka ginin ba a daidaita shi da kyau ba. Akwai kuma zargin amfani da kayan aiki marasa nagarta da ma'aikata wadanda ba kwararru ba.
"Don haka, FCTA za ta dauki abin da muhimmanci kuma ta tuntubi hukumomin da abin ya shafa don kawo karshen abin kunyar nan."
Gini mai bene biyu ya rufta ya danne mutane da dama a Abuja
Tunda farko, mun kawo muku cewa mutane da dama sun makale sakamakon ruftawar ginin a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng