Emefiele Ya Cinna Wa Dajin Wuta da Sunan Kama ’Yan Tsirarun Beraye, Cewar Shehu Sani
- Tsohon sanata a Najeriya ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke shan wahala wajen samo sabbin kudade da aka buga a kasar
- Shehu Sani ya ce gwamnan CBN ya cinnawa daji wuta da sunan kama wasu 'yan tsirarun beraye a daji
- Ya misalta hakan ne saboda gwamnatin Najeriya ta ce ta kawo batun sauyin kudi saboda kama 'yan rashawa a kasar
Najeriya - Sanata Shehu Sani ya koka kan yadda ‘yan Najeriya ke cikin kunci ta yadda ake ganin karancin sabbin Naira a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a jihar Kaduna, inda ya ce ka’idojin da gwamnan CBN Godwin Emefiele ya kawo na sauya kudi na cutar da talakawa.
A cewarsa, an samu tashin hankali da rikicin tattalin arziki bisa wannan doka da aka kawo mai guba da nufin tsoma ‘yan kasa cikin wahala da kunci.
A cewar Shehu Sani, CBN ta zama wata cibiyar siyasa da ke kokarin kawo tsaiko ga tattalin arzikin Najeriya a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsaloli na matsin tattalin arziki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Garin kama barayi ana kuntatawa ‘yan Najeriya
Da yake magana kan yadda za a kawo hanyar kwamushe masu rashawa, Shehu Sani ya ce:
“Idan gwamnatin Buhari na son kama ‘yan rashawa, ba sai ta jira har zuwa wannan lokacin ba kuma ba sai ta fake da kuntatawa talakawa ba. Emefiele ya cinnawa daji wuta da sunan kama ‘yan tsirarun beraye."
Ya kuma siffanta yadda Najeriya ta sayta zuwa wani sansanin ‘yan gudun hijira da mutane ke layi don cire kudadensu a bankuna, Daily Post ta ruwaito.
Shahararren Sarki Ya Ragargaji Emefiele, Ya Ce Ƙarancin Takardun Naira Barazana Ne Ga Rayuwan Yan Najeriya
A cewarsa:
“’Yan Najeriya na cikin tashe-tashen hankula na fafutuka don samo kudi, neman kudin, hankoron ganin kudi da yin komai don kudi.”
Ya tuna cewa, ‘yan Najeriya na siyan dalar Amurka a kasuwar bayan fage a bayan a kan farashi mai tsada, a yanzu kuma abin ya dawo kan kudin kasar; Naira.
Ya kuma zargi Ahmad Lawan da gaza tabuka komai wajen bincike da sanya CBN saboda wasu dalilai da suka shafi kasuwanci.
A bangare guda, wasu 'yan Najeriya sun fara sabawa da sabuwar dokar kudi, wani mai rake har ya fara karbar kudi ta POS.
Asali: Legit.ng