Daga Karshe: Khalifa Sanusi II Yayi wa Gwamna Ortom Martani Kan Kisan Makiyayan Nasarawa

Daga Karshe: Khalifa Sanusi II Yayi wa Gwamna Ortom Martani Kan Kisan Makiyayan Nasarawa

  • Sarkin Kano na 14 kuma Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi martani ga Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom kan kisan makiyayan Nasarawa
  • Sanusi yace tuni sun san cewa daga makurdi aka shirya ruwan wutar da aka yi kan makiyaya Nasarawa, idan ba haka bane, ya bari a yi bincike
  • Ya koka kan yadda fadar shugaban kasa tayi burus kan kisan ba tare da tayi jaje ko ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa

Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II, yayi martanin kan zargi da Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai yayi masa, Daily Trust ta rahoto.

Muhammadu Sanusi II
Daga Karshe: Khalifa Sanusi II Yayi wa Gwamna Ortom Martani Kan Kisan Makiyayan Nasarawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Alhamis, Ortom ya zargi cewa, wasu jama'a karkashin jagorancin Sanusi sun yi yunkurin shirya kai masa farmki kan kisan makiyaya a jihar Nasarawa.

Orrtom yace ana zarginsa da hannu cikin luguden wutan da ya halaka manoma masu tarin yawa a Kwateri, wani yanki tsakanin Binuwai da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Sanusi Lamido Sanusi Na Kitsa Shirin Kasheni, Gwamna Ortom na Benue Ya Koka

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma a tattaunawar da yayi da BBC Hausa, Sanusi yace Fulbe Global kungiyoyi na makiyaya ba kungiyar makasa ba wacce ke bada kariya ga al'adun Fulani tare da dawo da kyawawan dabi'un da aka san makiyaya dasu, neman musu hakkokinsu yayin da suke yaki da bata gari cikin kungiyar.

Ya zargi Gwamna Ortom da makarkashi ga makiyayan ta hanyar kirkiro da dokokin yaki da kiwo tare da kafa jami'an tsaro jiha da ke yaki da makiyaya.

Yace:

"Gwamna Ortom ne aka san ya zo da dokokin hana Fulani kiwo da kirkiro da masu gadin dabbobi a Binuwai tare da basu makamai.
"Sun halaka Fulani, sun kwace musu shanu. Sun tatse su tare da matsanta musu. Wannan ba zargi bane kawai.
"Ni tare da Lamidon Adamawa da marigayi Ahmed Joda mu ka gana da mataimakin shugaban kasa, IG na lokacin Idris, ministan harkokin noma Audu Ogbeh inda na gabata da takarda ga wadanda ke wurin.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Yiwa Tsohon Sarkin Kano Sanusi Wankin Babban Bargo

"Na fallasa cewa gwamnatin jihar Binuwai za ta horar da masu tsaron dabbobin yadda za su yi amfani da makamai don karya dokokin Najeriya. Gwamnatin Najeriya ta san da wannan amma ba ta iya yin komai ba."
"Wadannan mutanen an basu makamai kuma sun halaka mutane da basu da laifi tare da kwace shanunsu. Lamarin baya-bayan nan da ya faru a Nasarawa ba shi ne na farko ba.
"Wannan shi ne kusan karo na biyar da suka jefe bam kan wadannan jama'ar. Daga gwamnan Nasarawa har sarakunan gargajiya babu wanda yayi magana kan suna da 'yan ta'adda a zo a halaka su.
“Duk luguden wuta da aka yi a Nasarawa an shirya ne a Makurdi. Dole ne a kama shi da laifi tun mun san matsayarsa kan Fulani. Bincike ne kawai zai wanke shi daga dukkan zargi.
"Me yasa ba za a yi bincike a bankado wanda ya shirya luguden wuta ba da wanda ya ba sojin saman umarnin kaddamar da hakan?

Kara karanta wannan

2023: Abinda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Faɗa Wa Atiku Yayin da Ya Je Kamfe Sakkwato

"Mun rubuta budaddiyar wasika ga shugaban kasa. Har yanzu babu wata takarda da ta fito daga fadar shugaban kasa ta na ta'aziyya ga wadanda lamarin ya ritsa da su balle a basu diyya. Fadar shugaban kasa tayi shiru, da a ce a kudu ne aka kashe mutum 1, sai sun yi magana."

- Sanusi ya koka.

Na gama jajantawa wanda ya rasa yara 9 da shanu 70 ana jajiberin mutuwar Hassan, Gwamna Sule

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yace mutuwar 'dansa jarabawa ce daga Allah domin gwada imaninsa.

Ya bada labarin yadda ya dinga rarrashin bawan Allah da yayi rashi yara 9 da shanu 70 sakamakon luguden bam da sojin sama suka yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng