Yan Bindiga Sun Kashe A Kalla Mutum 6,000 A Jiha Ta, In Ji Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji

Yan Bindiga Sun Kashe A Kalla Mutum 6,000 A Jiha Ta, In Ji Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi ikirarin cewa yan bindiga sun kashe mutane sama da 6,000 a jihar tun daga shekarar 2017
  • Ortom ya zargi gwamnatin tarayya da rashin yin abin da ya dace wajen magance matsalar yan bindigan, ya kuma ce jihar na da ‘yan gudun hijira miliyan biyu
  • Ortom ya musanta cewa yana adawa da kowace kabila kuma ya ce kowa yana bin doka iri daya, ciki har da yan kabilar Tiv, wadanda aka kama aka gurfanar da su a gaban kuliya bisa dokar hana kiwo a fili

Jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce yan bindiga sun kashe mutane fiye da 6,000 a jiharsa tun shekarar 2017, rahoton The Cable.

Benue na cikin jihohi masu yawa da ake yawaitan samun hare-haren yan bindiga da sace mutane da kashe-kashe.

Kara karanta wannan

Hukumar yan sanda ta yi magana game da mutumin da ya mutu a layi ciki banki

Gwamna Ortom
Yan Bindiga Sun Kashe A Kalla Mutum 6,000 A Jiha Ta, In Ji Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji. Hoto: @daily_trust
Asali: Depositphotos

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya dade yana zargin gwamnatin tarayya ta rashin yin abin da ya kamata don magance matsalar yan bindigan.

Da ake magana da shi a wata hira a Arise TV a ranar Juma'a, Ortom ya yi ikirarin cewa akwai mutum miliyan 2 da suka rasa muhallinsu a jiharsa.

Ya ce:

"Lokacin da ka ke da yan bindiga barkatai, kuma babu wanda ke kokarin taka musu birki kuma suna kashe mutane kullum.
"Kwana uku da suka wuce, an kashe DPO. Babu satin da bana rasa mutum 10. Tun 2017, yan bindiga sun kashe mutum 6,000. Ina da mutanen da suka rasa muhallinsu fiye da miliyan 2."

Ortom ya zargi Sanusi daukan nauyin kai masa hari

A ranar Alhamis, Ortom ya yi ikirarin cewa wasu mutane karkashin jagorancin tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi, sun zarge shi da aikata wasu abubuwa da nufin neman dalilin kai masa hari.

Kara karanta wannan

Ina Tare Da 'Aladu' Ne Lokacin Da Na Soki Tinubu, Fani-Kayode

An ce an masa zargin ne saboda artabu da Ortom ya dade yana yi da makiyaya a kasar.

Da ya ke martani kan zargin, gwamnan ya ce baya da matsala da wata kabila, yana mai cewa doka daya ce ke kan kowa a kasar ba tare da la'akari da kabila ba.

Ortom ya ce:

"Ni ne mutum na farko da na fara alakanta fulni da laifi? Ba ka ji abin da Sultan ya fada ba a baya kan yan bindiga a Najeriya? Ba ka ji abin da gwamnan Katsina ya fada ba? Ko gwamnan Taraba?"

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164