Tsadar Mai Da Naira: A Tausayawa Talaka, a Tausaya Wa Al'umma: Gwamnan Bauchi ga Gwamnatin Tarayya

Tsadar Mai Da Naira: A Tausayawa Talaka, a Tausaya Wa Al'umma: Gwamnan Bauchi ga Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnan Bauchi ya shiga sahun masu fada aji da suka koka kan irin bakar wahalar da jama'a ke sha
  • Bala Abdulkadir ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tausaya al'umma saboda ba su ji da dadi
  • Yan Najeriya a fadin tarayya na layukan bankuna don ajiye kudadensu ko kuma samun sabbin kudi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammad Abdulkadir, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dubi Allah sannan ta duba halin da talakawa suka shiga sakamakon sauya fasalin Naira.

Gwamnan wanda aka fi sani da Kauran Bauchi ya ce mutane basu tsira da wahala da tsadar man fetur ba, gashi yanzu ko kudin sayan man babu.

Kaura ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Kada ku sake kara wa'adin daina amfani da Naira, Atiku ga CBN

A cewarsa:

"Baya ga wahalar ƙaranci da tsadar man fetur, kalanzir da iskar gas da aka shafe fiye da shekara a ciki musamman a nan Arewa, al'uma na cikin matsanancin ƙunci sakamakon canjin kuɗi.
A mafi yawancin wurare babu tsoffin kuɗaɗen balle sabo, kafin a same su kuma sai an sha baƙar azaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da wannan nake kira ga gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya da su samar da hanyoyin sauƙaƙa samar da kuɗaɗen ga bankuna da al'uma don ba su damar cigaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum."
Kauran Bauci
Tsadar Mai Da Naira: A Tausayawa Talaka, a Tausaya Wa Al'umma: Gwamnan Bauchi ga Gwamnatin Tarayya Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Jami'an tsaro suyi aikinsu

Gwamna Bala ya kara kira ga jami'an tsaro su dau mataki kan yan sana'ar POS masu taimakawa wajen azabtar da mutane.

Muna kira ga hukumomin tsaro da su sanya ido, zaƙulo tare da hukunta jami'an bankuna da masu sana'ar POS dake ɓoye sabbin takardun kuɗi ko sayar da su domin hakan ya saɓawa dokar ƙasa da zamantakewa.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Ɗan Takarar Shugaban Kasa Da Zai Marawa Baya a 2023

A tausaya wa talaka!

Atiku Abubuakar na PDP yace bai amince da kara wa'adin daina amfani da tsaffin Naira

Atiku Abubakar, ya yi kira ga bankin CBN kada ya sake dage wa'adin daina amfani da tsaffin takardun Naira.

Atiku, a jawabin da ofishin kamfensa ya fitar ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa bankin ya fitar da isassun sabbin kudi cikin al'umma

Asali: Legit.ng

Online view pixel