Shahararren Sarki Ya Ragargaji Emefiele, Ya Ce Ƙarancin Takardun Naira Barazana Ne Ga Rayuwan Yan Najeriya

Shahararren Sarki Ya Ragargaji Emefiele, Ya Ce Ƙarancin Takardun Naira Barazana Ne Ga Rayuwan Yan Najeriya

  • Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi, wani basaraken gargajiya a Osun, ya soki yadda yan Najeriya ke shan wahala saboda chanjin kudi
  • Basaraken yace babban bankin kasa CBN bai bi matakan da ya dace ba kuma ya kamata ya nemi yafiyar yan Najeriya
  • Basaraken ya bukaci a duba hanyoyi da za a kawar da wahalar da wahala suke sha aka tabbatar kudin ya shiga hannun jama'a

Osun - Wani basaraken a Osun, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi a ranar Laraba ya zargi gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emifiele da jefa yan Najeriya cikin wahala sakamakon karancin sabbin takardun kudi a fadin kasar, Tribune ta rahoto.

Basaraken wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Osogbo ya bayyana cewa fara amfani da sabbin kudin ya durkusar da al'amuran kasuwanci da dama a Najeriya, yana mai cewa irin wannan a hankali ake bi don saukaka harkokin kasuwanci.

Kara karanta wannan

Assha: Na Kusa Da Buhari Sun Fi Damuwa Da Batun Sauyin Kudi, Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ke Ransa

Abdulrasheed Adewale
Shahararren Sarki A Najeriya Ya Caccaki Emefiele, Ya Ce Karancin Takardun Naira Illa Ne Ga Rayuwar 'Yan Adam. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya yi takaicin sabon kudin ya jefa yan Najeriya a wahala sosai. Ya durkusar da harkokin tattalin arzikin kasa. Kullum kara ta'azzara lamarin ya ke. A matsayina na mai fada aji, dole inyi magana'.
''Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emifiele na bukatar ya nemi yafiyar yan Najeriya kan wahalar da ya jefa su. Har yanzu ban gamsu da sake fasalin kudi ba tare da anbi hanyar da ta dace wajen tabbatar da wadatar sabon kudi ba. Mummunar illa ne ga kawa zucin dan Adam.
''Ya kamata Emefiele ya sake yi wa yan Najeriya bayani kan dalilin chanja kudi da kuma kayyade wa'adi ba tare da isassun kudi na kewayawa ba. Ba zamu zuba ido mu cigaba da shan wahala ba. Hakan ba daidai bane a halin da ake ciki saboda INEC za ta bukaci kudi don tura kayan aiki''.

Kara karanta wannan

Wahala Ta Kare, CBN Ya Ba Da Sabon Umarni Na Yadda Za a Ba 'Yan Najeriya Sabbin Kudi

Oba Akanbi ya kira ga masu ruwa da tsaki musamman gwamnatin tarayya da ta sake duba wannan kudiri duba da irin wahalar da yan Najeriya da su ji ba basu gani ba ke sha ta kuma tabbatar ta sanya ido don tabbatar da zagayen kudi.

Da yake karin bayani, abin da yake faruwa yanzu, shiri ne don a cusa kiyayyayar mulkin shugaba Buhari a zuciyar yan kasa, basaraken ya ce, yan Najeriya sun shiga birgici, fargaba da kuma yunwa saboda karancin takurdun kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164