Yan Sanda Na Neman Wani Mutum Ruwa A Jallo Saboda 'Bidiyon Bindiga' A Legas
- Yan sanda na Jihar Legas sun ayyana neman wani Tajudeen Olanrewaju Bakare ruwa a jallo kan mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba da barazana
- Hakan na zuwa ne bayan fitar wani bidiyo a dandalin sada zumunta da ya nuna shi yana dauke da bindigu, yana yi wa al'umma barazan
- Kakakin yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin ya gargadi sauran wadanda ke nufin aikata laifi su bar jihar domin ba za a raga musu ba
Jihar Legas - Rundunar yan sandan jihar Legas ta ayyana neman wani Tajudeen Olanrewaju Bakare, ruwa a jallo saboda yin barazana ga zaman lafiya da mallakar bindiga ba tare da bin ka'ida ba.
An ga Bakare, wanda aka fi sani da Oba Ogboni Abalaiye Ajamajebi a wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta a baya-bayan nan yana rike da bindiga yana kuma yi wa mutanen yankin Surulere barazana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, a cikin wata sanarwa da ya fitar a sahihin shafinsa na Twitter ya ce:
"Tawagar CSP Egbeymi ta RRS, bisa aiki kan bayanan sirri ta kai samame a gidan wani mutum a Surulere a jihar.
"An tsinci bindigu guda uku a gidansa, kunshin harsashin Beretta guda daya, harsashi 9mm daya, wasu harsasai da hoton wanda ake zargin."
Rundunar yan sandan na Legas ta gode wa mutanen jihar saboda sanya ido kan al'amurra tare da sanar da jami'an tsaro a kan lokaci.
Ta kuma gargadi dukkan masu nufin tada rikici su bar jihar domin duk wanda aka samu da hannu wurin aikata laifi zai dandana kudarsa bisa tanadin doka.
Yan sanda sun kama wata mata da ake nema ruwa a jallo yayin da ta ke neman shiga aikin yan sanda
A wani rahoton daban mun kawo muku cewa an cafke wata mata da yan sanda ke nema ruwa a jallo a, New jersey, Amurka.
An kama Zyeama Y. Johnson ne a ranar 4 ga watan Oktoba yayin da ta halarci wurin wani abu da ta yi tunanin gwaji ne na daukanta aiki.
Bugu da kari, matar ta nemi shiga aikin ne a wani sashi da suka kware wurin binciken mutanen da ake nema ruwa a jallo.
Asali: Legit.ng