Wata Mata Da Yan Sanda Ke Nema Ruwa A Jallo Ta Shiga Hannu Yayin Neman Shiga Aikin Yan Sanda

Wata Mata Da Yan Sanda Ke Nema Ruwa A Jallo Ta Shiga Hannu Yayin Neman Shiga Aikin Yan Sanda

  • Wata mata mai suna Zyeama Y. Johnson ta saukaka wa yan sanda sun kama ta bayan ta kai kanta ofishinsu
  • Zyeama wacce yan sandan ke nema ruwa a jallo saboda laifuka ta nemi aikin ne a ofishin yan sanda na Hudson County, New Jersey
  • Bayan yan sandan sunyi duba sunanta, sun gayyace ta tattaunawa da sunan za a dauke ta aiki amma tana zuwa aka kama ta

Amurka - An kama wata mata da yan sanda ke ne nema ruwa a jallo bayan ta shigar da takardar neman aiki a matsayi mai gadi a ofishin yan sanda, Linda Ikeji ta rahoto.

An kama Zyeama Y. Johnson ne a ranar 4 ga watan Oktoba bayan ta halarci abin da ta yi tunani gwaji ne kafin daukanta aiki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan sa'o'i 7, 'yan sanda sun kamo daya daga wadanda suka yi fashi a Abuja

Suspect
Wata Mata Da Yan Sanda Ke Nema Ruwa A Jallo Ta Shiga Hannu Yayin Neman Shiga Aikin Yan Sanda. Hoto: Linda Ikeji
Asali: Facebook

Abin mamaki, ta nemi aikin a ofishin yan sandan New Jersey, USA, a sashin da suka kware wurin binciko mutane da ake nema ruwa a jallo.

Wani dan sanda a ofishin Sheriff na Yankin Hudson ya shaida wa Newsweek cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ta nemi aiki a matsayin mai gadi, kamar yadda aka sani a yayin bincikarta, mun duba ko tana cikin wadanda ake nema."

Kakakin ofishin yan sandan ya ce:

"A lokacin, sai muka kira ta amsa tambayoyi - ko abin da ta yi tunanin amsa tambayoyin aiki ne da ofishin yan sanda a matsayinta na wacce ke tserewa daga doka."

Yan sandan Monroe, Pennsylvania suna neman Johnson ruwa a jallo saboda almundaha, da wasu rashin kai kanta kotu saboda saba dokokin tuki a Jersey City.

Shugaban yan sanda Sheriff Frank Schillari ya shaidawa shafin NJ.com cewa bayan kama Johnson, an bincika kayanta.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Gayyaci Mutum 5 Kan Mutumin Da Ake Rufe Tsirara Na Fiye Da Shekaru 20 A Kaduna

Laifukan da ake zargin Johnson da aikata wa

An gano katin cire kudi a banki guda biyu da aka taba kai rahoton cewa an sace su, kuma aka gurfanar da ita kan satar katin cire kudi na ATM.

A yanzu ana tsare da Johnson a gidan yari na Hudson da ke Kearny inda take jira a mayar da ita Pennsylvania.

Ba wannan ne karon farko da yan sanda ke kama wanda suke nema ruwa a jallo ba bayan sun nemi aiki a hukumar yan sandan.

A watan Agusta, an rahoto cewa an taba kama wani a kasar Africa ta Kudu da aka kama bayan ya tafi caji ofis don bincika batun neman shiga aikin dan sanda.

Ya shafe shekaru bakwai ana nemansa ruwa a jallo kan satar kayayyaki.

An Kama Matar Da Ta 'Sace' Tagwaye Bayan Mahaifiyarsu Ta Ki Sayar Mata Da Su

A wani rahoton, hukumar hana fatauci mutane, NAPTIP, reshen Makurdi ta kama wata mata yar shekara 49, Mrs Augustina Ikyor, kan mallakar wasu tagwaye a jihar, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da aka ga bidiyon mata mai juna biyu na leburanci a wurin wani gini

Kwamandan hukumar na shiyyar, Bai Iveren, cikin wata sanarwa, ta ce mahaifiyar tagwayen ta yi ikirarin cewa wacce ake zargin ta kwace jariran ne daga wurin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel