Wata Uwa Ta Koma Kula Da Mutum-mutumi Saboda Diyarta Mai Shekaru 21 Ta Ki Haifa Mata Jika
- Wata matashiya ta nuna abun ban dariya da mahaifiyarta ta yi saboda bata haifa mata dan jikkale ba
- Mahaifiyar tata wacce ta matsu ta nemo mutum-mutumi sannan take bashi kulawa tamkar dan gaske, lamarin da ya ba matashiyar mamaki
- Bidiyon mahaifiyarta tana kula da dan mutum-mutumin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da mutane suka bayyana ra’ayinsu
Wata matashiyar budurwa ta garzaya soshiyal midiya don wallafa wani bidiyo na mahaifiyarta da ke nunawa dan mutum-mutumi da ta siya gata.
A cewar matashiyar, mahaifiyarta wacce ta matsu ta yanke shawarar samo mutum-mutumi saboda ta ki ta haifa mata jika.
A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano mahaifiyar tata tana shirya wani dan mutum-mutumi tamkar dan gaske kuma ta yi biris da diyar tata wacce ke daukar bidiyonsu.
Da take bayanin bidiyon, matashiyar ta dauki abun da mahaifiyar tata take a matsayin abun dariya, tana mai cewa shekarunta 21 kacal a duniya kuma ba ta tare da kowani namiji.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta ba mahaifiyarta hakuri, cewa ita din yarinya ce karama har yanzu. Ta rubuta a bidiyon:
"Yi hakuri hajiya, ni karamar yarinya ce kuma ina farin ciki."
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
arieslovexx ta ce:
"Kuma kada ki bari wani ya matsa maki ki haifi da har sai kin shirya dari bisa dari sannan ki nemawa dan uba nagari."
K.DRAMA-queen ta ce:
"Aww hakan ya yi kyau. mahaifiyata bata ga nata jikan ba har yanzu. shekaru shida kenan da aka haife shi mun yi nesa sosai da juna."
Sarah ta ce:
"Saboda idan aka zo kan batun rainon jikan da ake magana a kai ne za su ce "na rigada na gana rainon nawa 'ya'yan."
Pearledbluntsss ta ce:
"A'a kada ki yi mun zancen jika sai dai idan za ki kula da su na kwanaki 5 a mako daya."
Yan sanda sun gurfanar da ango saboda ya kara aure
A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Lagas ta gurfanar da wani magidanci bisa zarginsa da kara aure a kan aure da kuma bayar da bayanan karya.
Asali: Legit.ng