Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira: Atiku Ya Aika Sako Mai Karfi Ga Gwamnan CBN Emefiele

Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira: Atiku Ya Aika Sako Mai Karfi Ga Gwamnan CBN Emefiele

  • Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci babban bankin kasa da yayi buris da masu kukan karin wa'adin chanjin kudi
  • Dan takarar shugabancin kasar ya bukaci babban bankin kasa CBN da ya fito da karin hanyoyi don wadatar sabon kudi a hannun mutane
  • Atiku ya kuma bayyana cewa takaita buga takurdu da kuma dogara da tsarin takaita kashe kudin takarda abune mai kyau ga tattalin arzikin kasa

Dan takarar shugabancin kasa a inumar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Laraba, ya bukaci babban bankin kasa CBN da kada su kara wa'adin chanjin kudi idan wa'adin 10 ga watan Fabrairu ya cika.

Ya ce, hakan, ya zama dole idan dai har ana son cimma munufa da kuma dalilin da yasa aka sauya fasalin kudin, rahoton The Punch.

Atiku da Emefiele
Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira: Atiku Ya Aika Sako Mai Karfi Ga Gwamnan CBN Emefiele. Photo credit: Atiku Abubakar, Godwin Emefiele
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Bayyana 'Yan Najeriya Kwanakin da Za a Kwashe Kafin Matsalar Sabbin Kudi Tazo Karshe

Dalilin da yasa Atiku ke son CBN kada ta tsawaita wa'adin dena karbar tsaffin naira

A wata sanarwa da ta fito daga Abuja ranar Laraba daga ofishin yakin neman zaben sa, Atiku ya bukaci babban bankin da ya sake yin duba kan matakan da yake bi wajen raba kudin don tabbatar da waduwar zagayen sabuwar takardar Naira.

Sanarwar ta ce:

''Karin kwana goma zai bawa mutanen mu na karkara da kuma sauran mutane a fadin kasar nan damar mayar da tsofaffin kudin su zuwa bankuna. Zai kuma taimakawa babban bankin don samun damar rarraba sabbin kudin ga bankuna don mutane su samu damar amfani da kudin.
''A cikin wannan kwana goman, ina rokon CBN da ya fito da maslaha kan matsalolin da mutane ke fuskanta wajen chanja tsohon kudinsu da sabo a kuma kara hanyoyin isar kudin zuwa jama'a. Babban bankin zai iya duba yiwuwar buga karin wasu sabbin kudin don kawar da matsalar karancin kudin a hannun daidaikun mutane, musamman mazauna karkara da suke da bukatar kudi don amfanin yau da kullum."

Kara karanta wannan

Toh fa: Ba a isa a hana mu sabbin kudi ba, talaka ne mai shan wahala, inji Kwankwaso

Sanarwar ta cigaba da cewa:

''Idan CBN yana tunanin sun kammala shiri kuma dole bankuna suyi aiki a ranakun hutun karshen mako don magance matsalar mutane da kuma mazauna karkara, ya kamata ta duba yiyuwar hakan, tun da kudin da wannan mutane ke nema ba wani mai yawa bane.
"Babban abu a nan shine tabbatar da cewa kudin ya zagaya ko ina ta yadda mutane za su samu cikin sauki. Kowacce doka da za ta amfani jama'a dole ya zama ta girmama bukatar su kuma ya zama mutane ba su sha wahala ba.
''Amma, babban bankin ya toshe kunne kan manyan da ke matsa lamba da koke-koke kan lallai a sake kara wa'adi wanda hakan ka iya kawo kuma baya kuma ba abin karba bane. Ina goyon bayan gina tattalin arzikin kasa kan takaita kashe takardun kudi da kuma takaita yawan buga kudin."

Ba wannan lokacin ya dace a sauya fasalin takardun naira ba, El-Rufa'i

Kara karanta wannan

Kada ku sake kara wa'adin daina amfani da Naira, Atiku ga CBN

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya soki sauyin takardun naira da CBN ta yi yana mai cewa ba wannan lokacin ya dace a yi ba.

Ya amince da cewa manufar mai kyau ne amma sai dai lokacin da aka zabi yin canjin ya yi kama da wani mataki na son bata wa jam'iyyar APC suna a wurin mutanen kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164