Kotun Koli Ta Kori Bwacha a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Taraba a Jam’iyyar APC
- Kotun koli ta kori dan takarar gwamnan APC a jihar Taraba bisa gano dambarwa a zaben fidda gwanin da aka gudanar
- Wannan na zuwa ne bayan da kotun daukaka kara ta mai zama a Yola ta yi watsi da hukuncin korar dan takarar a baya
- A baya, babbar kotun tarayya ta soke zaben fidda gwanin gwamnan APC da aka gudanar a jihar ta Taraba
FCT, Abuja - Kotun koli ya soke zaben Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Taraba, TheCable ta ruwaito.
Da suke yanke hukunci a ranar Laraba, alkalai biyar na kotun koli karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun sun tabbatar da hukuncin kotun tarayya na soke zaben fidda gwanin gwamnan Taraba na APC.
A watan Satumban bara, kotun tarayya a Jalingo ya soke zaben fidda gwanin gwaman APC da ya samar Bwacha a matsayin dan takarar APC.
Yadda batun shiga kotu ya faro
David Sabo Kente, daya daga cikin ‘yan takarar gwamnan APC ne ya maka Bwacha a kotu, inda ya kalubalanci sahihancin nasararsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Simon Amobeda, alkalin kotun tarayya da ke zama a Jalingo ya amince da bukatar wanda ya shigar da kara cewa, ba a yi sahihin zaben fidda gwanin gwamna a Taraba ba.
Ya kuma yi Allah-wadai da fitar da sakamakon karya da baturen zabe ya yi a filin jirgi tare da cika wandonsa da iska zuwa kasar waje ta yi a a lokacin da aka yi zaben na fidda gwanin gwamna.
Alkalin ya umarci a sake sabon zaben fidda gwanin gwamnan APC a jihar cikin kwanaki 14, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Hukuncin baya-bayan nan
Sai dai, a ranar 24 ga watan Nuwamban bara, kotun daukaka kara a birnin Yola ya yi watsi da hukuncin babbar kotun da ta kori Bwacha.
Amma duk da haka, Kente bai saduda ba, ta hannun lauyansa Kanu Agabi ya sake shigar da kara a gaban kotun koli.
A hukuncinta na yau, kotun koli kuwa ta kori Bwacha tare da rusa zaben, inda kotun yace an tafka kuskure a zaben na APC.
A halin da ake ciki dai, kotun koli ya yi watsi da batun kotun daukaka kara, ya tabbatar da hukuncin babbar kotun tarayya.
Asali: Legit.ng