CBN Ya Gano Sabbin Kudi Har Miliyan N4m Makare a Cikin Bankuna a Ogun

CBN Ya Gano Sabbin Kudi Har Miliyan N4m Makare a Cikin Bankuna a Ogun

  • Babban banki CBN ya ce ya kama wasu bankunan kasuwanci da laifin ɓoye sabbin kuɗi kimanin miliyan N4m
  • Mataimakin Daraktan sashin kula da bankuna, Mista Makinde ya ce zasu ɗauki matakin da ya dace a kansu
  • A cewarsa CBN ya gama aikin bangarensa, duk wannan wahalar da ake sha laifin bankuna ne

Ogun - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ya gano naira miliyan N4m na sabbin takardun kuɗi da aka ɓoye a bankunan kasuwanci a jihar Ogun.

Mataimakin Daraktan sashin kula da al'amuran banki na CBN reshen jihar, Kayode Makinde, shi ne ya bayyana haka ranar Talata yayin da ya fito sa ido kan yadda tsarin raba sabbin kuɗin ke tafiya.

Babban banki CBN.
CBN Ya Gano Sabbin Kudi Har Miliyan N4m Makare a Cikin Bankuna a Ogun Hoto: premiumtimesng
Asali: Facebook

Babban ma'aikacin CBN ɗin, wanda ƙarara ya nuna fushinsa, ya zargi Bankunan kasuwanci da yi wa kokarin babban banki na samar da isassun kuɗin ga al'umma zagon ƙasa.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Gwamnan CBN Ya Tona Asiri Kan Sabbin Kudi, Ya Faɗi Babban Laifin Bankuna

Jaridar Premium Times ta rahoto Mista Makinde na cewa bankuna na cin amanar CBN yayin da yake kokarin ganin mutane sun samu sabbin kiɗin cikin sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin daraktan CBN ya ƙara da cewa wannan mako na uku kenan da fara shirin sa ido da CBN ya ɓullo da shi domin tabbatar da bankuna na bin ƙa'idojin raba wa jama'a sabon kuɗi.

Idan baku manta ba yan siyasa sun zargi gwamnan CBN da kokarin hana ruwa gudu wajen sakin kuɗi su isa hannun al'umma saboda wani kudirinsa na siyasa.

Manya a siyasar ƙasar nan na ganin cewa CBN ya ɓoye takardun naira ne domin gurbata babban zaɓe mai zuwa a watan Fabrairu da muke ciki da Maris.

Shin ina matsalar take?

Amma a jawabinsa, Mista Makinde, ya faɗa wa yan Najeriya cewa kar su zargi kowa da laifi sai bankunan kasuwancin, inda a cewarsa CBN ya sauke hakkinsa.

Kara karanta wannan

Hankali Ya Kwanta: CBN Ya Magantu Kan Yawan Sabbin Kudi, Ya Faɗi Yadda Kowane Ɗan Najeriya Zai Samu

Yace:

"Wannan mako na uku kenan na kokarin bin diddigin tabbatar da ana bin umarnin CBN dangane da baiwa mutane sabbin kuɗi. Muna da bankuna, wakilai da wakilai na musamman dake aikin musanya kuɗin."
"Lamarin ne akwai sarƙaƙiya, mun ga masu boye sabon kuɗin, mun tilasta masu sun zuba a ATM, wasu kuma basu da tsari mai kyau. Daga abinda muka gani, ba CBN ce mai laifi ba illa bankunan kasuwanci."
"Mun kama wasu da sabbin kudin a ajibge, mun matsa masu su sanya a na'urar ATM, mun gaya masu maimakon su aje, su sanya a ATM kuma su tuntubi cibiyar samar da tsabar kuɗi wacce tana da hurumi kai tsaye ta nemi ƙari daga CBN."

Wane mataki CBN zai ɗauka kan irin waɗannan bankunan?

Babban ma'aikacin CBN ya yi bayanin cewa sun ci karo da masu cin amana kuma zasu kai Kes din zuwa gaba domin ɗaukar matakin da ya dace a kansu.

Kara karanta wannan

An Samu Cigaba: CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa Ga Masu Cire Sabbin Kudi a ATM

"Mun je wani ɗaya daga cikinsu (Bankuna) da ya gaza mana bayanin inda miliyan N4m na sabon kuɗin suka yi, ba zamu bar abun haka nan ba zamu hukunta su."

A wani labarin kuma CBN ya jaddada cewa akwai isassun sabbin takardun kuɗi da zasu wadata kowane ɗan Najeriya

A cewar babban bankin, abu ɗaya da bankuna zasu yi a basu kuɗin nan take shi ne su tura bukatar sabbin kudi ga CBN .

Daraktan sashin bincike na cikin gida a CBN, Lydia Alfa, ta yi kira ga 'yan Najeriya kar su daga hankulansu kan rashin sabbin kuɗin musamman a yanzu da aka kara wa'adin musaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262