Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe
- Nasir El-Rufa'i ya bayyana ra'ayinsa game da lamarin tsadar mai da wahalar Naira dake gudana
- Gwamnan na Kaduna ya tabbatar da abinda Tinubu ya fada kwanaki baya na cewa ana yi masa zagon kasa
- Duk da kara wa'adin daina da amfani da tsaffin Naira, yan Najeriya na cigaba da fama da wahala
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya bayyana cewa akwai wasu yan tsiraru a fadar shugaban kasa da basu son dan takaran shugaban kasan APC, Bola Tinubu, ya ci zaben bana.
El-Rufa'i ya bayyana hakan a shirin Sunrise Daily, na gidan talabijin Channels ranar Talata.
Duk da bai bayyana sunayen wadannan yan tsiraru ba, ya ce har yanzu suna jin haushi saboda wanda suke so ba shi yayi nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC ba.
Ya ce suna amfani da Shugaba Muhammadu Buhari wajen cimma manufofinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
"Ina ganin akwai wasu yan tsiraru a fadar shugaban kasa da suke son mu fadi zaben nan saboda basu samu abinda suke so ba; suna da nasu dan takaran da suke so kuma bai yi nasara a zaben sharen fagge ba."
"Suna kokarin ganin mun fadi zabe, kuma suna amfani da shugaban kasa saboda yana son yin abinda ya dace."
"Zan baku misalai biyu; kan tallafin man fetur wanda ake kashe tiriliyoyin Naira kai, kuma muka yanke shawarar a cire."
"Misali na biyu shine na sauya fasalin kudi. Ku fahimci shugaban kasa. Yana da niyya mai kyau. Amma yin hakan a wannan lokacin bai da wani amfani ga tattalin arziki ko siyasarmu."
Jawabin El-Rufa'i ya biyo bayan jawabin Bola Tinubu wanda yace fadar shugaban kasa na son ganin ya fadi zabe shiyasa aka bijiro da wahalar mai da sauya fasalin Naira.
Kalli bidiyon:
Tinubu ya sake caccakan gwamnatin Buhari
Karo na biyu, jiya a birnin Calabar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kira gwamnatin shugaba Buhari mara tunani da nazari kan lamarin tattalin arziki.
Tinubu ya ce gwamnatin Buhari ta samu Naira a N200 ga Dalar Amurka amma yanzu farashin ya tashi zuwa har N800.
Ha yanzu dai hadiman Buhari da na APC basu fadi komai game da wannan jawabi ba.
Asali: Legit.ng