Matar Da Ta Auri Saurayin 'Diyarta Bata Aikata Laifin Komai Ba: Hisbah Ta Yanke Hukunci
- Hukumar Hisbah ta fitar da sakamakon binciken d ata gudanar kan labarin wata mata a jihar Kano
- Labarin Malama Khadija ya karade kafafen ra'ayi da sada zumunta a makon da ya gabata
- Kwamandan Hisbah ya baiwa mutane shawara su nemi ilimin addini maimakon yada jita-jita
Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano a ranar Talata tayi fashin baki game da kace-nace kan auren matar da ta aure tsohon saurayin 'diyarta a karamar hukumar Rano ta jihar.
Kwamitin Hisbah wacce tayi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin ta gabatar da rahoton bincikenta da yammacin Talata, 31 ga Junairu, 2023, rahoton Punch.
Yayin gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Hussain Ahmed, ya yi bayanin cewa kwamitin ta gano an yi wannan daurin aure bisa doka kuma an cika dukkan sharruda.
Ya yi bayanin cewa Khadija Rano ta rabu da tsohon mijinta kuma ta kammala iddanta na watanni uku kamar yadda addinin Musulunci ya bukata, sannan ta auri tsohon saurayin diyarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'in na Hisbah ya yi watsi da jita-jitan cewa Khadija na soyayya da saurayin diyarta tun kan mutuwar aurenta, da kuma cewa ta tilasta mijinta ya saketa don ta auri wani.
Ya ce wannan aure ya bi tsarin dokar shari'ar Musulunci kuma hakan ne dalilin da yasa kwamandan Hisbah na Rano ya daura auren.
Jawabin kwamandan Hisbah na jiha
Kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, ya jinjinawa kwamitin bisa gudanar da aiki yadda ya kamata, riwayar Vanguard.
Ibn Sina ya yi kira ga al'umma su daina ya'da labarun karya kuma su nemi ilimin addinin Musulunci.
Ni ba jahila bace, na son me na gani na auri saurayin 'diyata, Malama Khadia
Malama Khadija, matar da labarinta ya yadu ta rabu da mijinta don auren saurayin 'diyarta ta yi jawabi da labarinta dake yaduwa da kuma dalilin da yasa tayi hakan.
Wannan abu ya auku ne a karamar hukumar Rano ta jihar Kano.
Malama Khadija ta ce ita fa tana jin dadin aurenta da sabon miji kuma tana cikin koshin lafiya.
Hukuncin addini kan lamarin
Diraktan makarantar Islamiyya a birnin tarayya Abuja, Malam Abu Aamir, ya bayyana cewa addini bai haramtawa mace auren wani namiji ba muddin ba muharraminta bane.
A cewarsa, kasancewar mutumin tsohon saurayin diyarta ba sharadi bane na hanata aurensa muddin ta kammala iddarta kafin suka fara soyayya.
Asali: Legit.ng