Karancin Sabbin Naira Ya Sa ’Yan Najeriya Sun Fara Amfani da CFA a Wasu Yankunan Kasar
- Yayin da samun sabbin kudi ya zama aiki ga wasu ‘yan Najeriya, sun gano hanya mafi sauki don ci gaba da harkokin kasuwanci
- Mutanen jihar Sokoto sun koma amfani da kudaden CFA domin biyan bukatunsu na kasuwancin yau da kullum
- An ruwaito yadda lamarin ya faru da kuma yadda suke harkalla bayan sauya kudin Najeriya a kwanakin baya
Jihar Sokoto - Wasu mazauna jihar Sokoto sun koma amfani da kudin CFA a madadin Naira don ci gaba da harkallolin da ke gabansu na yau da kullum.
Wannan na zuwa ne a lokacin da gwamnatin Najeriya ta yi sauyin wasu kudade tare da ba da wa’adin daina amfani da tsoffi.
Idan baku manta ba, an buga sabbin N200, N500 da N1000 a Najeriya watan Disamban bara don kawo mafita ga wasu matsalolin tattalin arziki da tsaro a kasar.
Dalilin da yasa wasu mutanen Sokoto suka fara amfani da CFA
A cewar rahoton RFI, karancin manyan sabbin kudin Naira da kuma kayyade adadin da za a cire ne ya kawo wannan lamari tsakanin ‘yan kasuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ake zantawa da wani dan kasuwa, Alhaji Rila da ke kasuwanci a tsohuwar kasuwar Sokoto, ya bayyana yadda ‘yan kasuwa a jihar suka gano mafita ga wannan karancin kudi da addabar jama’a.
Ya shaida cewa, ‘yan kasuwan na ci gaba da samar da sabbin dabaru domin gudanar da kasuwancinsu cikin aminci, ciki kuwa har da amfani da CFA.
Darajar CFA ya yi kasa
A bangare guda, an ce farashin CFA ya sauka kasancewar jama’a a yankin na ci gaba da hada-hada da kudin ba kakkautawa.
A nasa bayanin, wani dan kasuwa mai suna Junaidu ya ce tuni ‘yan kasuwa suka fara bullo da dabarun warwarre matsalolin kudi don ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
A cewarsa, suna amfani da hanyoyi da yawa ta yadda ba za su dogara da takardun Najeriya ba ganin suna da alaka mai karfi ta cinikayya tsakaninsu da ‘yan Nijar.
A daya daga cikin harkallolin kasuwancin yankin, an ce ‘yan kasuwar wayar salula na karbar kwamutsen Naira da CFA tun bayan fara wannan rikici na karancin sabbin kudi.
Hukumomin gwamnati a Najeriya na ci gaba da kama wadanda ke boye sabbin kudi tare da siyar dasu a madadin musaya.
Asali: Legit.ng