An Hana Mutane Marasa Katin Zabe Shiga Fadar Babban Sarki A Najeriya

An Hana Mutane Marasa Katin Zabe Shiga Fadar Babban Sarki A Najeriya

  • Wani basaraken gargajiya a Osun ya yace ga duk mai son shiga fadar sa zai gabatar da katin zaben sa
  • Sarkin Oluwa na Iwo ya ce katin zaben na da matukar muhimmanci kuma yana taimakawa cigaban kasa
  • Kwamishinan zaben Osun ya bayyana a shirye suke su gudanar da zaben gaskiya kuma mai inganci irin sa na farko

Jihar Osun - Oluwa na Iwoland, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi, ya bayyana ranar Talata cewa ga duk wanda ke son ziyartar fadar sai ya gabatar da katin zaben sa.

Ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da ya ke karbar bakoncin kwamishinan zaben Jihar Osun, Dr Mutiu Agboke, Daily Trust ta rahoto.

Katin zabe
An Hana Mutane Marasa Katin Zabe Shiga Fadar Babban Sarki A Najeriya. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Assha: INEC ta hango matsalar da ka iya kaiwa ga lalata shirin zaben 2023

Oluwa ya bayyana cewa yawan masu kada kuri'a yana da alfanu ga siyasa kuma cigaban tattalin arziki, yana mai karfafawa yan kasa da kuma kungiyoyi da suyi aiki da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ''don tabbatar da an karbi ragowar katin zaben da suka rage ba a karba ba.''

Basaraken ya bayyana cewa:

''Zan fara tambayar katin zabe ga duk wanda ya ziyarci wannan fadar don neman taimako.
''Ya kamata mu sanya sharadin da zai tilasta mutane karbar katinan Zabe. Karbar katin zabe daya daga cikin manyan abubuwan da zasu maida mutum cikakken dan Najeriya matukar ka haura shekara 18. Kada kuri'a zai kara tabbatar da zaman ka dan kasa mai kishi.''

Ya kuma shawarci INEC da ta isar da sakon shi ga ma'aikatanta, musamman na wucin gadi.

A hukunta duk wanda ya taimaka wurin magudin zabe, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi

Oluwa ya kuma bayyana cewa duk wanda ya taimaka ko ya dauki nauyin magudin zabe ya kamata a hukunta shi.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Buhari Bai Yi Magana Kan Kisan Fulani Da Bam Ba, Allah Wadai Wallahi: Miyetti Allah

A cewarsa:

''Duk wani ma'aikacin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da yake taimakawa wajen magudin zabe da kuma sauya alkaluma yana jawowa kansa tsinuwar Allah, ba ma iya kansa ba har al'umma. In ka goyi bayan magudi, to hakika ka gayyato tashin hankali.
''Magudin zabe a koda yaushe yana janyo koma baya ga dimukradiyya da kuma cigaban tattalin arzikin kasa. Dan kasa nagari bazai taba goyon bayan ko wani irin magudi ba. Mu zama mutanen kirki a ayyukanmu.''

Tun da fari, Agboke ya tabbatarwa da alummar Osun za a gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci kuma irin wanda ba a taba irinsa ba, yana rokon Oluwa da ya sanya baki don mutane su karbi katinan zaben su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164