Jami'an DSS Sun Yi Rama da Masu Siyar da Sabbin Takardun Naira

Jami'an DSS Sun Yi Rama da Masu Siyar da Sabbin Takardun Naira

  • Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun cafke wasu jama'a da ake zargi da siyar da sabbin takardun Naira da Najeriya ta canza
  • Duk da jami'in hulda da jama'a na DSS< Peter Afunanya bai sanar da sunaye ko inda aka kama su ba, yace hukumar za ta cigaba da zakulo su
  • Ya sanar da cewa wannan haramtacciyar harka ce kuma dukkan hukumomin tsaro zasu tashi tsaye kan miyagun da ke zagon kasa ga tattalin arziki

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama wasu jama'a da suka shirya kansu suna siyar da sabbin takardun Naira da aka canza.

Peter Afunanya, jami'in hulda da jama'a na hukumar DSS ne ya tabbatar da hakan a takardar da ya saki ranar Litinin, jaridar TheCable ta rahoto.

Gwamnan babban bankin Najerya
Jami'an DSS Sun Yi Rama da Masu Siyar da Sabbin Takardun Naira. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Shugaban Kasar Rasha Ya Tura Yan Matan Gidan Rawa 100 Faggen Yaki Don Sanyaya Zukatan Sojoji

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da hukumar tsaron ta farin kaya bata bayyana sunaye da inda aka kama wadanda ake zargin ba, hukumar a takardar da ta fitar a ranar Litinin tace wasu ma'aikatan bankunan 'yan kasuwa na taimakawa harkar.

Wannan takardar ta samu sa hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar DSS, Peter Afunanya, wanda ya ja kunnen cewa hukumar za ta bi lungu da sako don damko masu hannu a harkar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Takardar tace:

"Huklumar tsaro ta farin kaya na sanar da jama'a cewa ta kama wasu jama'a da suke siyar da sabbin takardun Naira. A yayin da suke aiki a wasu sassan kasar nan, an gano cewa wasu ma'aikatan bankunan 'yan kasuwa ke taimakawa wannan zagon kasa ga tattalin arzikin.
"A don hakan, hukumar na jan kunnen masu wannan harkar da su guji yin ta. Hukumomin da suka dace na daidaito a wannan harkar, ana kira ga su da su tashi tsaye wurin kula da duba ayyukan wandan miyagun.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hukumar Yan Sanda Ta Kama 'Yar TikTok, Murja Kunya A Kano

“A sani kuma, hukumar ta umarci jami'anta da su tabbatar da cewa duk wani mutum ko kungiyoyi da ke wannan harkar an zakulo su. Don haka, duk wanda ke da bayanai da zasu yi amfani ya mika su ga hukumomin da suka dace."

Ana siyar da tsabar sabbin kudi a Zaria, Kaduna

A wani labari na daban, an gano yadda wasu jama'a a tashar motar Dadi da ke garin Zaria ta jihar Kaduna suke siyar da sabbin takardun Naira.

A kowacce bandir din 'yan dubu daya-daya, ana siyar da ita kan N130,000 yayin da ta N500 ake siyar d aita kan N70,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng