Shugaban Kasar Rasha Ya Tura Yan Matan Gidan Rawa 100 Faggen Yaki Don Sanyaya Zukatan Sojoji

Shugaban Kasar Rasha Ya Tura Yan Matan Gidan Rawa 100 Faggen Yaki Don Sanyaya Zukatan Sojoji

  • Vladimir Putin ya tura runduna ta musamman faggen yakin Ukraine domin taya Sojoji yaki
  • Wannan runduna ce ba bindiga suke dauke da shi ba, runduna ce ta yan mata tsala-tsala
  • Ranar 24 ga Febrairu zai cika shekara guda da fara yaki tsakanin kasar Rasha da makwabciyarta Ukraine

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya bada umurnin tura yan mata da yan gidan rawa faggen yaki domin sanyaya zukatan mazajen fama dake yaki da kasar Ukraine.

Wannan na shirin shirin murnar cika shekara guda da fara yakin Rasha da Ukraine.

Putin ya yiwa wannan umurni da sunan 'rundunar soji na musamman' watau yan matan, rahoton DailyStar.

An umurci kwamandojin su shirya sharholiya wa jami'an Sojojin.

Sama da yan mata 100 za'a tura cikin jirage a Donbas inda za'a kwashe kwanaki biyar ana hutu da sharholiya.

Kara karanta wannan

Yar Haya Ta Kashe Mai Gida Ta Hanyar Matse 'Ya'yan Marainansa A Ogun

Ptuin
Shugaban Kasar Rasha Ya Tura Yan Matan Gidan Rawa 100 Faggen Yaki Don Sanyaya Zukatan Sojoji
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani jami'in sojan Rasha mai matsayin Kanar ya bayyana hakan a shafin ra'ayi da sada zumunta.

Sojan wanda aka yiwa lakabin 'armoured death' ya ce:

"Za'a shiryawa jarumanmu Casu na musamman tare da yan mata yan rawa, barasa da abinci don nuna godiyanmu bisa bautar da suke wa kasar."
"Za'a shirya wasu taruka lokacin hutun domin sanyaya zukatan sojoji da suka kasance suna faggen fama."

Putin Ya Bada Umurnin A Dakatar Da Yaki Da Ukraine, Ya Bayyana Dalili

Kwanakn baya kun ji Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya umurci ministan tsaro na kasar ya bada umurnin tsagaita wuta a yakin da ake da Ukraine saboda kirsimetin 'gargajiya'.

Za a fara tsagaita wutan ne cikin awa 36, za ta fara aiki daga ranar 6 ga watan Janairu, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wata Mata Mai Shayarwa Ta Jefar Da Jinjirinta Yayin Tserewa Daga Yan Bindiga A Neja

Bisa al'ada, mutane da dama na bikin kirsimetin 'gargajiyan' ne a ranakun 6 da 7 na watan Janairu.

A cewar kafar watsa labarai na Kremlin, Putin ya yi sanarwar ne bisa kiran da cocin Rasha ta yi a baya na neman a tsagaita wuta lokacin bikin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel