CBN Ta Tantance Wakilai 400 Da Zasu Dakile Yawon Tsaffin Kudi

CBN Ta Tantance Wakilai 400 Da Zasu Dakile Yawon Tsaffin Kudi

  • Babban bankin Najeriya ya ɗauki matakin musanya wa mutane kudadensu a ba su sabbin da aka canja
  • CBN ta tantance wakilai 400 waɗanda zasu shiga lungu da sako domin musanya wa mutane kiɗi a sassan jihar Kogi
  • Daraktan dabaru na CBN ya ce sabon tsarin da suka zo da shi zai taimakawa mutane su iya ma'amala da kuɗin Intanet

Kogi - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya baiwa wakilan kuɗi 400 lasisin aiki da nufin saukaƙawa yan Najeriya mazauna karkara hanyar samun sabbin takardun kuɗi a lungu da sako na jihar Kogi.

Babban bankin ya ce wannan zai taimakawa mutane da dama su musanya kuɗaɗensu kafin wa'adin 31 ga watan Janairu da za'a rufe karɓan tsoffin kuɗi ya cika.

Babban bankin Najeriya.
CBN Ta Tantance Wakilai 400 Da Zasu Dakile Yawon Tsaffin Kudi Hoto: dailytrust

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Daraktan sashin dabaru na CBN, Clement Buari, ne ya bayyana haka ranar Asabar a fadar Elulu na Mopa, Oba Julius Olufunsho Joledo.

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Ya ce daga yanzu kowane mutum na da ikon zuwa Bankuna ko wurin waɗan nan wakilan domin ya musanya tsoffin kudinsa da sababbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan ya ƙara da cewa kowane mutum ɗaya na da ikon musanya N10,000 na tsaffin kuɗi domin a ba shi sabbin kudi kuma kyauta.

Buari ya ce:

"Mutane zasu iya aje tsaffin kuɗinsu a Asusun Banki, haka nan waɗanda ba su da Asusun Banki za'a karfafa musu guiwa su buɗe sabo a wurin wakilan musanya kuɗi."
"Manufarmu taƙaita yawon takardun kuɗi, za'a wayar da kan jama'a su koma amfani da kuɗin Intanet da CBN ta ɓullo da shi."
"Wannan shirin na musayar kuɗi shi ne na farko a tarihi da aka kirkiro domin mutanen da basu mu'amala da Bankuna a ƙananan hukumomi 13 na Kogi, inda ba banki ko na'urar cire kuɗi ATM."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Ganduje Ya Ɗage Ziyarar da Buhari Zai Kawo Kano Kan Abu 1 da Ya shafi Canjin Kuɗi

Tsohon gwamnan Kogi, Chief Clarence Olafemi, wanda ya yi jawabi a madadin Basaraken, ya roki CBN ya duba ƙara wa'adi daga 31.ga wata, musamman saboda mutanen karakara.

Sabbin Kudi sun rage yawan sace mutane da neman kuɗin fansa, CBN

A wani labarin kuma Babban Banki ya bayyana cewa da yuwuwar canja kuɗi sun rage yawan ta'addanci a Najeriya

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele yace mai yuwawa sabon tsarin ya rage wa yan ta'adda karfin karɓan kudin fansa saboda ba'a amsar tsoffi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262