Ban Yi Nufin Tsanantawa Talakawa Da Lamarin Sauya Fasalin Naira Ba: Buhari
- Karon farko, shugaban kasa ya baiwa yan Najeriya hakuri kan lamarin sauya fasalin Naira
- Shugaban kasan bayan komawa Abuja daga jihar Katsina ya ce bai nufi baiwa talakawa wahala da lamarin ba
- Ya yi alkawarin cewa za'a yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa takardun Naira sun yawaita
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da yan Najeriya su kwantar da hankulansu game da lamarin sauya fasalin Naira da kuma wa'adin daina amfani da tsaffin takardun Naira.
Buhari ya ce zai tabbatar da cewa al'umma da kasuwancinsu basu wahala ba kuma kowa zai samu sabbin kudi cikin 'kankanin lokaci.
Buhari ya bayyana hakan yayin martani kan wahalan da yan Najeriya ke yi wajen layi a bankuna don mayar da tsaffin kudadensu.
Hakan ya biyo bayan jawabin dan takarar kujerar shugaban kasa, Bola Tinubu, inda yace masu mulki sun boye Naira don ya fadi zabe.
Garba Shehu ya ruwaito Buhari da fadin haka a jawabin da fitar ranar Asabar, 28 ga Junairu, 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Masu boye kudi na nufa, Buhari
A cewarsa, attajirai masu boye aka nufi dakilewa ba talaka ba.
Ya jaddada cewa sauya fasalin Naira ya zama wajibi saboda dakile masu buga kudin jabu, yan rashawa, yan ta'adda da kuma karfafa tattalin arziki.
Ya ce yana sane da wahalar da talakawa ke ciki saboda yan kudaden kashewa da suke ajiyewa a gida, saboda haka zai tabbatar da cewa ya share musu hawaye.
Ya ce babban bankin Najeriya da bankuna na kokarin tabbatar da cewa an fito da sabbin kudade domin rabawa mutane.
Hakazalika za su yi duk ami yiwuwa wajen kawar da halin kuncin da mutane ke ciki.
Martanin yan Najeriya
Yan Najeriya cikin gaggawa sun yi tsokaci game da jawabin Shugaba Muhammadu Buhari.
Da dama sun ce yi masa addu'an Allah ya taimaka yayinda wasu masu yawa kuma suka ce ya ji tsoron rajamun da mutane suka yi masa a Katsina ne.
Tuni dai hukumar yan sandan jihar Katsina ta karyata rahoton cewa an yiwa shugaban kasan ihun bamaso ko rajamu yayinda ya tafi kaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar Katsina ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng