'Dan Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Kwanta Dama, Hankula Sun Tashi

'Dan Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Kwanta Dama, Hankula Sun Tashi

  • A safiyar Juma'a 27 ga watan Janairu 2023 ne gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Injiniya Abdullahi A. Sule ya rasa ransa bayan wata gajeriyar jinya
  • Hassan Abdullahi Sule ya kwanta dama ne bayan watanni bakwai da shan shagalin aurensa da masoyiyarsa, lamarin da ya tada hankula
  • An ruwaito yadda jama'a da dama suke ta dandazon mika sakonnin ta'aziyyarsu ga mai girma gwamnan jihar Nasarawa da fatan dacewa da aljannar Firdausi a matsayin makoma
  • Jama'a sun siffanta mutuwar Hassan AA Sule, 'dan gwamnan a matsayin babban rashi ba ga jihar kadai ba harma da kasa baki daya

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule ya rasa 'dansa, Alhaji Hassan AA Sule a safiyar Juma'a.

Hassan AA Sule
'Dan Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Kwanta Dama, Hankula Sun Tashi. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Vanguard ta tattaro yadda Hassan ya kwanta dama bayan wata gajeriyar jinya. Sai dai, an fara mika sakonnin ta'aziyyar 'dan gwamnan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan Takarar Gwamna a Fitacciyar Jihar Arewa Ya Kwanta Dama Bayan Fama da Rashin Lafiya

A wani sakon ta'aziyya da mai jaridar Eggonnews, Matthew Kuju ya sa hannun gami da bayyana wa Vanguard a Lafia da misalin karfe 5:30 na safe, ya nuna:

"Zuciyoyinmu sun cika da radadi bayan gano yadda muka rasa 'danmu, Hassan. Amma shakka babu, akwai tsananin zafi idan uba ya birne 'dansa, sai dai Allah ne ke kaddara hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna rokon Allah ya tashesa cikin bayinsa na kwarai, sannan yasa aljannar Firdausi ce makomarsa, muna rokon Allah ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa."

A wani sako da ya yi kama da haka, Mai girima 'dan majalisar da ke wakiltar mazabar Arewacin Lafia a majalisar jihar Nasarawa Hon. Barr. Muhammad Ibrahim Alkali ya ce cike da mamaki ya samu labarin rasuwar 'dan mai girma gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Hassan Abdullahi Sule.

A sakon ta'aziyyar ga mai girma gwamnan jihar Nasarawa, 'dan majalisar ya siffanta mutuwar 'dan gwamnan a matsayin babban rashi ba ga jihar Nasarawa ba har da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Katsina: Matasa SUn Balle Zanga-zanga Jim Kadan Bayan Buhari ya Kaddamar da Gadar Sama a Kofar Kaura

Hon. Alkali ya roki Ubangiji ya gafarta ma marigayin kurakurensa sannan yasa aljanna ce makomarsa.

"Ina mika sakon ta'aziyyata ga mai girma gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Injiniya Abdullahi A. Sule, bisa rasuwar dansa Alhaji Hassan. Ina rokon Allah (SWT) ya sanya sa a aljannar Firdausi sannan ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa"

- Kamar yadda takardar ta bayyana.

A ranar 25 ga watan Yunin 2022 Hassan ya angwance da masoyiyarsa Salamatu Muhammad wanda aka daura auren a fadar Sarkin Keffi, shagalin auren da fitattun 'yan Najeriya suka halarta, Sahara Reporters ta rahoto.

Jarumi kuma furodusa Awarwasa ya riga mu gidan gaskiya

A wani labari na daban, fitaccen jarumi kuma furdusa a masana'antar Kannywood, Abdulwahab Awarwasa ya kwanta dama.

Ya rasu bayan doguwar jinyar da yayi inda ya bar matar aure daya da 'ya'ya uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel