Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Dira Wurin Hakar Ma'adanai, Sun Halaka Mutum 5
- Mutanen Hayin Udawa cikin karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna sun shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka yi dirar mikiya mahakar ma'adanai gami da budewa mahakan wuta
- An ruwaito yadda a kalla mahaka ma'adanai biyar suka rasa rayukansu yayin da sauran suka samu raunukan harsasai daban-daban a farmakin
- Kamar yadda sarkin yankin ya bayyana, wurin da lamarin ya auku bashi da nisa da inda hatsabiban suka yi kwantan bauna ga jami'an NSCDC inda suka halaka 7 daga ciki
Chikun, Kaduna - A kalla masu hakan ma'adanai biyar ne suka rasa rayukansu bayan 'yan bindiga sun kutsa wajen mahakar ma'adanai a Hayin Udawa cikin karamar hukumar Chikun da ke jihar.
Daily Trust ta rahoto cewa, lamarin ya faru jiya da rana yayin da 'yan bindiga suka hari masu aiki a mahakar ma'adanai.
Wani shugaban yankin a anguwar wanda ya bayyana kansa da Muhammadu Umaru ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Duk da babu cikakken bayani game da asalin abun da ya faru, amma wadanda lamarin ya ritsa dasu 'yan kauyen Udawa ne kamar yadda majiyoyi daga yankin suka bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Biyar daga cikin mahaka ma'adanan mu ne suka rasa rayukansu ranar Laraba, yayin da suke aiki a jeji. Dukkansu daga anguwar Udawa. Dama suna zuwa jeji ne don hako ma'adanai amma akwai saura da suka samu raunukan harsasai."
- A cewarsa.
Daily Trust ta rahoto cewa, ya kara da bayyana yadda wurin da aka kai harin bashi da nisa daga wurin da 'yan bindiga suka yi kwantan bauna ga jami'an hukumar tsaron farar hula (NSCDC), inda suka halaka bakwai daga ciki da mahaka ma'adanai shida wasu makwanni da suka shude.
Duk kiraye-kirayen waya da aka yi waa kakakin 'yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige bai amsa ba.
Fusatattun matasan Katsina sun balle zanga-zanga kan zuwan Buhari
A wani labari na daban, matasa a jihar Katsina sun barke da zanga-zanga jim kadan bayan shugaba Buhari ya kaddamar da gadar Kofar Kaura.
Fusatattun matasan sun dinga jifa tare za ihun bamu yi kan jami'an tsaro da kuma motocin APC da ke wucewa.
Tuni jami'an tsaron suka saki barkonon tsohuwa ganin cewa lamarin yana neman yin kamari.
Asali: Legit.ng