Dalilin Da Yasa Na Zabi Atiku Kan Peter Obi, Naja'atu, Tsohuwar Hadimar Tinubu
- Hajiya Naja'atu ta bayyana cewa rashin kyakkyawan manufa ne ya hanata goyi bayan Obi a zabe mai zuwa
- Ta bayyana cewa ana bukatar kyakkyawan tsari da kuma hadin gwiwar kowanne yanki don kaiwa nasara a zaben Najeriya
- Jigo a tafiyar Tinubu, Hajia Naja'atu Mohammed ta bayyana cewa abu ne mai sauki banbance tsari mai nagarta
Tsohuwar direkta, a kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC mai mulki, Naja'atu Mohammed, tayi bayanin dalilin da ya sa ta koma goyon bayan dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, maimakon dan takarar LP, Peter Obi a babban zabe 2023.
Naja'atu ta bayyana dalilanta yayin da take amsa tambayoyi a shirin safiya da gidan talabijin na Arise.
Naja'atu: Rashin kafuwa da sada zumunci a dukkan sassan kasar ya sa na zabi Atiku kan Obi
Ta bayyana rashin kafuwa, da kuma rashin fito da kyakkyawar alaka da sauran yankuna a matsayin abubuwan da za su hana Obi zama shugaban kasa ranar 25 ga Fabrairu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar Punch a baya-bayan nan ta rawaito cewa Naja'atu ta ajiye mukaminta na kwamitin yakin neman zaben APC.
Sai dai kwamitin yakin neman zaben Tinubu ya karyata ajiye mukamin nata, tare da bayyana cewa korar ta akayi sakamakon rashin bada gudunmawa a kwamitin.
Da take bayyana bayyana dalilin da yasa ta zabi Atiku a matsayin dan takarar da za ta goyawa baya, Naja'atu tace zabi ne tsakanin mutum mara nagarta da kuma mai nagarta tsakanin Tinubu da Atiku.
Ta ce:
''Ba wani abu ne yasa nake Atiku ba. Na bada dalilai na, a dalilai na na fada cewa, Peter Obi babu manufa a tsarinsa.
Yan Kwanaki Kafin Zabe, Tinubu Ya Daukarwa Iyaye Gagarumin Alkawari Da Zai Cika Masu a Kan 'Ya'yansu
''Na kuma bayyana cewa wannan ne karo na farko da matasan Najeriya suka hada karfi kuma suka fito don irin wannan tafiyar; ba ma a maganar Peter Obi. Wannan tsarin zai sa a manta da wani Peter Obi.
''Abin da nace shine suna da matsala a manufofinsu.
''Zan baku misali; tun 2003 Buhari yake samun kuri'a miliyan 15, amma baya cin zabe."
Ta cigaba da cewa:
''Meyasa? Duk da irin tarin goyon bayan yan Arewa da yake dashi, me ya hanashi yin nasara? Baiyi nasara ba saboda akwai matsala a manufofinsa kuma bai iya tsari ba.
''Sai da ya yi kyakkyawan tsari, wanda tun da farko yaki yadda musamman Kudu maso yamma, sannan ya zama shugaban kasa; wannan ne kadai dalilin.
''Saboda haka shiyasa ban bata lokaci ba don yin zabi tsakanin tsari mai nagarta da mara nagarta."
2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja
Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya gana da shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a Abuja
CAN tunda farko ta nuna cewa ba ta goyon bayan tikitin musulmi na musulmi na jam'iyyar APC ta yi bayan zaben Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa.
Asali: Legit.ng