Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Zaben 2023, Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Kiristoci A Najeriya

Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Zaben 2023, Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Kiristoci A Najeriya

  • An bukaci yan Najeriya kada kawai su zabi shugaban da ya dace amma shugaba da ke kaunar al'umma a zuciyarsa
  • Fasto Williams Kumuyi, Shugaban Cocin Deeper Life Bible Church, ya bukaci masu zabe su yi addu'a a yayin da zabe ke karatowa
  • A bangare guda, wasu shugabannin addini na da ra'ayin cewa babban zaben zai iya hada kan kasar ko tarwatsa ta, don haka dole kowa ya bada gudunmawarsa

Asaba, Jihar Delta - An bukaci kiristoci a Najeriya su yi aiki bayan addu'a gabanin babban zaben 2023 a kasar.

Babban Shugaban Cocin Deeper Life Bible Church, Fasto Williams Kumuyi, ya bada wannan shawarar a Asaba, babban birnin jihar Delta a ranar Laraba, 25 ga watan Janairun 2023, lokacin da ya isa garin don addu'a na kwana shida, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sai Yanzu Ka San Za Ka Zagi Buhari?, Atiku Ya Caccaki Tinubu

Kumuyi
Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Zaben 2023, Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Kiristoci A Najeriya. Hoto: W F Kumuyi
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Kumuyi ya aika da sakonni masu dauke da hikima ga kiristocin Najeriya

Ya ce:

"Muna addu'a don zaben amma dole mu yi aiki bayan addu'an bayan mun fito kwan mu da kwarkwata munyi zabe.
"Aiki wato mu fito kwanmu da kwarkwata mu jefa kuri'a, mu kasance masu hikima kada mu zabi shugabannin da ba su dace ba. Mu yi takatsantsan wurin zaben wanda za su mulke mu."

Shawara ga masu zabe da yan takara

Malamin addinin ya kuma yi kira ga masu kada kuri'a, su fito su sauke nauyin da ke kansu na yin zabe sannan ya kuma yi kira ga yan takarar su rika takatsantsan a harkokin su.

Ubangiji bai sanar da ni wanda zai maye gurbin Buhari ba, Malamin addini ya yi magana kan zaben shekarar 2023

Tunda farko, kun ji cewa babba limamin cocin na Deeper Life, Fasto Kumuyi ya ce kawo yanzu Ubangiji bai sanar da shi wanda zai lashe zaben shugaban kasa a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Ba Zamu Karba Kudin da Zasu Zama Takardun Tsire ba: 'Yan Bindiga Sun ki Karbar Tsofaffin N5.3m na Fansa a Kaduna

Amma ya yi alkawarin cewa idan nan gaba Allah ya masa wahayi game da babban zaben ba zai yi kasa a gwiwa ba zai sanar da yan Najeriya.

Kumuyi din ya sanar da hakan ne yayin wata zantawa da ya yi da yan jarida a Minna, babban birnin jihar Neja, yayin wani taro da suka yi a ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164