Sauya Kudi: Wa’adin CBN Zai Fi Shafar Al’ummar Karkara Ne, Inji El-Rufai

Sauya Kudi: Wa’adin CBN Zai Fi Shafar Al’ummar Karkara Ne, Inji El-Rufai

  • Gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci babban bankin kasa da ya kara wa'adin daina karbar tsoffin kudade a kasar
  • El-Rufai ya ce wannan mataki na CBN zai fi shafar al'ummar karkara ne saboda yawancinsu basu da bankuna
  • Da wannan ne gwamnan ya yi kira ga babban bankin Najeriya da ta kara wa'adin daina karbar kudaden

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa'adin daina karbar tsoffin takardun kudi cewa lokacin ya yi gajarta da yawa, rahoton Channels TV.

Babban bankin Najeriya dai ya ce za a daina amfani da tsoffin kudade a kasar daga ranar 31 ga watan Janairu lamarin da ya jefa al'umma musamman talakawa a halin wayyo Allah.

El-Rufai
Tsoffin Kudi: Wa’adin CBN Zai Fi Shafar Al’ummar Karkara Ne, Inji El-Rufai Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Babu bankuna a yawancin garuruwan karkara, El-Rufai

Kara karanta wannan

Shikenan: A Madadin Korafi, Zulum Ya Samo Hanyar da 'Yan Jiharsa Za Su Rabu da Tsoffin Kudi

El-Rufai ya bayyana cewa mutanen karkara da dama wadanda basu da hanyar yin hada-hada kudi sune wadanda wannan hukunci zai fi shafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi a wata hira da manema labarai a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna, gwamnan ya nanata cewa babu ta yadda za a yi manoman karkara da yan kasuwa a yawancin garuruwan jihar su cika wa'adin CBN na kai tsoffin kudinsu banki.

Ya bayyana cewa wasu kananan hukumomin basu da kowani banki a cikinsu, don haka ba a sako su cikin wannan tsari ba kenan.

Yayin da yake nuna goyon bayansa ga sauya kudin da CBN ya yi, El-Rufai ya bayyana cewa ya zama dole a baiwa mutanen yankunan karkara karin dama da za su sauya tsoffin kudadensu duk da cewar da ya yi damar da suke da shi dan kadan ne.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gwamnan CBN ya ki zuwa majalisa kan batun sabbin Naira, kakaki ya fadi matakin da zai dauka

Saboda wannan, gwamnan ya yi kira ga CBN da sauran bankuna da su samar da hanyoyin sauya tsoffin kudaden a garuruwan karkara.

Gwamna Babagana Zulum ya yi umurnin bude sabbin bankuna a Borno

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya umurci ma'aikatar kudi da ta gaggauta bude sabbin bankuna don yin kari kan wanda suke da shi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.

Hakan na daga cikin kokarin da gwamnan ke yi na tabbatar da ganin cewa al'ummarsa sun samu sauya tsoffin kudadensu kafin cikar wa'adin CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng