An Lakadawa Mawaki Duka, Yana Asibiti Saboda Kin Rerawa ‘Dan Takaran APC Waka

An Lakadawa Mawaki Duka, Yana Asibiti Saboda Kin Rerawa ‘Dan Takaran APC Waka

  • Kelvin Ibinabo yana zargin Machiavelli Ụzọ da wasu ‘yan dabar siyasa da yi masa mummunan duka
  • Mawakin ya ce Hadimin Gwamnan sun lallasa shi ne saboda ya ki rerawa ‘dan takaransu waka
  • Ụzọ yana cikin masu ba Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi shawara a karamar hukumar Ohaozara

Ebonyi - Shahararren mawakin nan da ke garin Ebonyi, Kelvin Ibinabo yana gadon asibiti a yanzu a sakamakon harin da Hadimin Gwamna ya kai masa.

Vanguard ta rahoto cewa Machiavelli Ụzọ ake zargi da laifin harin da aka kai wa mawakin.

Machiavelli Ụzọ yana aiki ne da Mai girma David Umahi a matsayin shugaban cibiyar Ohaozara Development Center da ke karamar hukumar Ohaozara.

Mawakin ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa Hadimin Gwamnan na jihar Ebonyi tare da wasu ‘yan daban siyasa ne suka lallasa masa duka.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Harbawa Mutane Bama-Baman Roka a Jihar Zamfara

Mawaki bai ji da dadi ba

A cewarsa, an rutsa shi da makamai, aka jibge shi, bayan nan sai suka rufe shi a wani daki. Kamar yadda fada, wannan ya faru ne a daren Ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta samu labari ‘yan sanda sun zo inda abin ya faru, suka cece shi a lokacin da ya yi raga-raga.

‘Dan Takaran APC
Taron yakin zaben APC a Ebonyi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yadda abin ya faru - Kelvin Ibinabo

Da yake bada labarin abin da ya faru, tauraron ya ce an gayyace shi yin wasa a wajen jana’izar surukar shugaban karamar hukumar Ohaozara a makon jiya.

Mawakin ya ce da maraice ya yi, sai ya bukaci abokan aikinsa su tattara kayan kida su bar wajen, a nan sai aka bukaci ya rerawa Francis Nwifuru waka.

Jaridar nan ta Tribune tc e Mista Francis Nwifuru babban ‘dan siyasa ne, shi ne ‘dan takarar Gwamnan jihar Ebonyi a karkashin jam’iyyar APC mai-mulki.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

Uzo ya dage sai mawakin ya yi wa ‘dan takaran waka, shi ya nuna ba zai yi ba domin su na kan hanyar zuwa Abakaliki ne, kuma ba siyasa ta kawo su ba.

Ibinabo ya ce da aka yi masa barazana sai ya dauki makirfon ya rera wakar ‘dan takaran, bayan ‘yan mintuna sai ya bari, amma aka ce bai isa ya tashi ba.

An rahoton mawakin yana cewa daga nan aka shiga lakada masa duka a wani gida, yanzu haka yana jinya a asibitin koyin aiki na Alex Ekwueme a Abakaliki.

An kai wa 'Yan LP hari

Rahoto ya zo cewa an aukawa Peter Obi da mutanensu a hanyarsu ta zuwa filin tashi da saukar jirgin, sannan aka sake rutsa tawagarsa da ruwan duwatsu.

Kwamitin neman takara ya bukaci jami’an tsaro su yi bincike saboda gudun haka ta sake faruwa.

Kara karanta wannan

Jirgin Sama Ya Yi Ɓarin Wuta Kan Jami'an Tsaro, Da Yawa Sun Mutu a Arewacin Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng