CBN Ya Maidawa Gudaji Kazaure Martani, Ya Fadi Inda Kudin da Ake Magana Suka Shiga

CBN Ya Maidawa Gudaji Kazaure Martani, Ya Fadi Inda Kudin da Ake Magana Suka Shiga

  • Gwamnan babban bankin Najeriya ya tabo batun harajin hatimi da bankuna suke karba a Najeriya
  • Godwin Emefiele ya ce a cikin shekaru shida, Naira biliyan 370.686 bankuna suka samu ba Tiriliyoyi ba
  • Hon. Muhammad Gudaji Kazaure yana zargin an yi awon gaba da fiye da Naira Tiriliyan 80 a CBN

Abuja - Godwin Emefiele wanda shi ne Gwamnan babban bankin CBN, ya musanya zargin da ake ji su na fitowa daga bakin Muhammad Gudaji Kazaure.

The Nation ta ce Gwamnan babban bankin kasar nan ya nuna cewa adadin kudin da bankuna suka samu daga harajin hatimi, bai kai abin da ake tunani ba.

Shi Hon. Muhammad Gudaji Kazaure yana ikirarin Naira tiriliyan 89 aka sace da asusun bankuna.

Amma da yake karin haske game da lamarin, Godwin Emefiele ya ce a cikin shekaru shida daga 2016 zuwa 2022, abin da aka samu Naira biliyan 370.6 ne.

Kara karanta wannan

Da walakin: CBN ya yi sabon batu game da karancin sabbin Naira da aka buga kwanan nan

An yi zaman MPC a Abuja

Rahoton The Cable ya tabbatar da cewa Mr. Godwin Emefiele ya fayyace hakan ne bayan an tashi taron kwamitin MPC da ya jagoranta a birnin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a ranar Talata, Emefiele ya jaddada bankin CBN bai rike da Naira tiriliyan 89.

CBN Abuja
Bankin CBN a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abin da ke cikin bankuna N44tr ne

Gwamnan babban bankin ya kara da cewa Naira tiriliyan 71 ne dukiyar da bankunan Najeriya suka mallaka, sannan Naira tiriliyan 44 ake da su a asusu.

Daga shekarar 2016 zuwa yau, harajin hatimi da aka karba ya kai Naira biliyan N370.686.

Hukumar tara haraji ta FIRS ta raba Naira biliyan N226.451 na kason zuwa asusun hadaka na FAAC, sai ragowar Naira biliyan N144.235 su na CBN.

Rahoton ya yi karin bayani cewa bankin FBN shi ya fi kowa tattaro wannan haraji a Najeriya, a tsawon shekaru shida ya iya tatso Naira biliyan 71.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanatan da Bai Taba Rike Sababbin N200, N500 da N1000 da CBN Ya Buga ba

Gwamnan na CBN ya ce sun dauko hayar kwararrun masu bincike domin a duba asusun, idan akwai kudin da aka boye, bankuna za su fito da su.

Zargin Gudaji Kazaure

A wata hira da aka yi da shi, an ji labari Muhammad Gudaji Kazaure ya zargi Gwamnan babban banki watau Godwin Emefiele da saye mutane.

Hon. Kazaure ya ce a boye ake kudunduno kasafin kudin CBN ba tare da ‘yan majalisa sun san komai ba, ya ce kasafinsu ya kai N4.2tr cikin shekaru uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng