Ba Gaskiya Bane, Akwai Sabbin Kudi a Bankuna, CBN Ya Karyata Jita-Jitar ’Yan Najeriya
- Babban bankin Najeriya ya ce akwai tarin kudade sabbi da ya buga a kasar nan, babu batun karancinsu a bankuna
- Wannan na fitowa ne daga bakin wani jigon a CBN a madadin gwamnan babban bankin a jihar Filato
- ‘Yan Najeriya an ci gaba da korafi da nuna damuwa bisa karancin sabbin kudaden da aka buga a kasar
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karyata ‘yan Najeriya bisa cewa da suke ana fama da karancin sabbin kudade a bankunan kasar nan, Vanguard ta ruwaito.
Hakazalika, ya umarci ‘yan kasa da su gaggauta kai kudadensu banki domin a ajiye musu ko kuma a basu sabbi don gujewa asara yayin da wa’adi ke kara gabatowa.
Gwamnan CBN, Mr. Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Jos, jihar Filato ta bakin daraktan fannin kula da biyan kudade na bakin, Musa Jimoh.
Ya bayyana cewa, saki fasalin da CBN ta yiwa Naira ya yi daidai ka ka’ida da tafarkin duniya na sauya fasalin kudi duk bayan shekaru biyar, duk a Najeriya an shafe shekaru tara ba ayi sauyin ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Baya ga koken 'yan Najeriya, majalisar wakilai ta kasa ta nemi CBN da ta duba yiwuwar kara wa'adin mayar da tsoffin kudaden kasar, rahotkn Punch.
Ku gaggauta sauya kudadenku
Da yake magana a ranr Talata a lokacin taron wayar da kan jama’a game da sabbin kudi, daraktan ya nanata cewa, sake fasalin N200, N500 da N1,000 aiki na gwamnatin kasar nan don magance matsalolin yawaitar kudi a hannun jama’a.
Ya kuma bayyana cewa, wannan sauyin zai magance ajiyar kudade da aka yi ba a juya su a kasar tare da rage yawan kudaden bogi.
Ya kuma bayyana cewa, sabbin kudaden suna nan tuli, kuma za su yadu ta hanyar ba da su a cikin bankunan kasuwanci da kuma ATM a fadin kasar.
Ya bukaci bankuna da su daina koron kudin tare da ba masu bukata don tafiyar da lamurra yadda ya dace.
An fara shirin musayar kudi
Ya kuma ambato shirin bankin na tura jami’ai da wakilai don yin musayar kudaden a bangarori daban-daban na Najeriya.
Ya shawarci duk wanda ya samu kudin da ke da wata nakasa da ya dawo dasu banki domin sauyawa nan take.
Ya kuma gargadi jama’a da cewa, kada su rudu ko CBN zai kara wa’adin da ya diba, domin babu wannan tunanin a kasa.
A ranar Talata din dai majalisar kasa tace za ta zanta da shugabannin bankuna don tattauna dalilin karancin kudi a bankunan kasar.
Asali: Legit.ng