Kotu Ta Umarci Mutum 6 Su Ba Wata Mata N1.5m Saboda Kiranta Mayya Kuma Munafuka a Jihar Kano

Kotu Ta Umarci Mutum 6 Su Ba Wata Mata N1.5m Saboda Kiranta Mayya Kuma Munafuka a Jihar Kano

  • Wasu mutane a jihar Kao za su biya tara mai tsanani bayan da suka kira wata mata mayya, munafuka kuma shegiya
  • Wannan na zuwa ne shekaru kusan uku da faruwar lamarin, inda aka kai batun gaban mai shari'a babban kotu
  • An kuma umarci su ba ta hakuri tare da bayyana neman afuwarta a bainar jama'a, hakazalika su fita harkarta

Jihar Kano - Wata babbar kotu mai zama a jihar Kano a ranar Talata ta umarci wasu mutum shida da su ba wata mata Sahura Sulaiman N1.5m a matsayin kudin bata sunan kiranta mayya, PM News ta ruwaito.

Karar da Sahura ta shigar na kalubalantar mutanen shida ne a hade wajen kakaba mata bakin suna ta hanyar kiranta mayya, munafuka kuma shegiya.

Wadanda aka shigar da karar a kansu sun hada da Rabi’u Wise, Talatu Salisu, Ummi Tasi’u, Mariya Musa, Nauwara Salisu, Aisar Gandu, Baba Umaru da wani boka Suwidi Habibu.

Kara karanta wannan

2023: Ku zabi mijina, Idan ya gaza laifi na ne, matar Atiku ta roki a hukunta ta

Yadda kotu ta hukunta wasu saboda kiran wata mata mayya
Kotu Ta Umarci Mutum 6 Su Ba Wata Mata N1.5m Saboda Kiranta Mayya Kuma Munafuka a Jihar Kano | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da take yanke hukunci, mai shari’a Zuwaira Yusuf ta ce, wadanda ake karan sun bata sunan Sahura, don haka dole su ba da kudin diyyar N1m don tada komada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ta umarce su da su ba Sahura karin N500,000 domin take hakkinta na dan Adam da suka yi.

Ku nemi afuwarta

A bangare guda, ta nemi su nemi afuwar matar a bainar jama’a a garin kana ta umarci da su fita daga harkarta kwata-kwata, Within Nigeria ta ruwaito.

A tun farko, lauyan mai shigar da kara, Mr. A I Muhammad ya shaida da cewa, wasu daga cikin wadanda Sahura ta maka a kotu surukanta ne, makwabta da boka.

Ya kuma shaida cewa, wannan lamarin ya faru ne a ranar 5 ga watan Yunin 2020 da misalin karfe 11:00 na safe a kauyen Burum Burum a karamar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Rayuka 2 na Matasan da Suka je Gyara Sokaway a Kano Sun Salwanta Bayan Sun Kasa Fitowa

Da yake martani ga hukuncin, lauyan wadanda ake kara, Mr. Nazifi Rabiu ya nemawa wadanda yake karewa sassaucin mai shari’a.

An daure alkalai bisa cin kudin mamaci

Shari'a a Najeriya bata tsaya kan talaka ba, kwanakin baya aka daure wasu alkalai a kasar bisa zargin sun saci kudin mamaci sama da miliyan 500.

Tuni wani rahoton da muka kawo a baya ya bayyana sunayen wadannan alkalai da suka gamu da fushin doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.