Fadawan Shehun Borno 4 Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota
- Mai martaba Shehun Borno ya yi rashin wasu hadiminsa guda hudu a wani mummunan hadarin da ya auku a jihar Borno
- An ruwaito cewa, mutum hudu ne daga fadawansa suka kone kurmus lokacin da suke kan hanyar zuwa Damaturu
- Hakazalika, an ce wasu mutum uku sun samu raunuka, ana ci gaba da ba su kulawar asibiti, sun tsira
JIhar Borno - An shiga tashin hankali da firgici yayin da wani mummunan hadari ya yi sanadiyyar mutuwar mutum hudu daga fadawan Mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai Elkenemy.
Rahoton da muke samu daga jihar Borno ya bayyana cewa, wannan mummunan lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Litinin 23 ga watan Janairun 2023.
Kafar labarai ta Zagazola Makama ta bayyana cewa, hakan ya faru ne a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu lokacin da motarsu ta kama da wuta.
Yadda lamarin ya faru
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa kafar cewa, mutum hudu da ke cikin motar sun mutu kurmus zuwa toka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai, an yi nasarar ceto mutum uku da ke cikin motar dauke da munanan raunukan da suka samu daga hadarin.
Ya zuwa yanzu dai majiya bata bayyana sunayen wadannan bayin Allah da suka riga mu gidan gaskiya ba tukuna.
Motoci 3 Sun Tafka Hatsari a Kwaryar FCT, Sun Take Jama’a da ke Kan Titi
A babban birnin tarayya Abuja kuwa, wasu mutum, takwas sun rasa rayukansu yayin wani hadarin mota da ya auku.
Wannan lamarin ya faru ne a titin Nnamdi Azikwe da ke babban birnin tarayya Abuja da misalin karfe 12 na ranar Lahadi.
Wani ganau ya shaida cewa, da idonsa ya kirga gawarwakin mutum takwas da suka rasa rayukansu a wannan mummunan hadarin da ya auku.
Ana yawan samun munanan hadurra a titunan Najeriya, hukumomi na danganta hakan da tukin ganganci na direbobi a kasar.
A bangare guda, wasu kuma na ganin gangancin gwamnati na kin gyara da inganta tituna a bangararori daban-daban na kasar da ke bukatar daukin gaggawa.
A nata bangaren, gwamnati na yawan ba da manyan ayyukan ginawa da gyaran tituna a bangarori daban-daban na kasar, kuma ana yin ayyukan.
Asali: Legit.ng