Motoci 3 Sun Tafka Hatsari a Kwaryar FCT, Sun Take Jama’a da ke Kan Titi

Motoci 3 Sun Tafka Hatsari a Kwaryar FCT, Sun Take Jama’a da ke Kan Titi

  • Shaidar gani da ido ta tabbatar da yadda rayukan mutum takwas suka salwanta sakamakon mummunan hatsarin da ya ritsa da motoci uku a Abuja
  • An gano cewa motoci uku ne suka yi karon gamo mu raba a mahadar Nicon kuma suka hada da wadanda ke tsaye suna jiran ababen hawa
  • Tuni jami’an FRSC suka kai dauki inda suka dinga kwashe wadanda lamarin ya ritsa dasu zuwa asibiti da kuma gawawwakin zuwa ma’adanarsu

FCT, Abuja - A kalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu a hatsarin da aka tafka a mahadar Nicon da ke kan titin Nnamdi Azikiwe a Abuja.

Hatsarin Mota
Motoci 3 Sun Tafka Hatsari a Kwaryar FCT, Sun Take Jama’a da ke Kan Titi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wannan lamarin ya faru wuraren karfe 12 na ranar Lahadi kamar yadda shaida ta sanar.

Bayanai kan hatsarin har yanzu ba su da yawa amma ganau mai suna Israel Adegboyega yace lamarin ya ritsa da wata Toyota, Camry da Mazda.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Halaka Basarake a Jihar Arewa, Gwamna Ya Kakaba Dokar Zaman Gida

Jama’ar da ke cikin motocin uku, masu jira su tsallake titin da masu jiran hawan ababen hawa zuwa wasu wurare ne lamarin ya ritsa da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shaidar gani da idon yace ya kirga gawar mutum takwas a kasa yayin da wasu uku aka tabbatar da mutuwarsu.

A kalamansa:

“Na kirga mutum takwas kwance a kasa yayin da na je wurin amma ina da tabbacin biyu zuwa uku sun mutu a take kafin in je wurin.
“Jama’a na ta tattara kafafu da sauran sassan jikin wadanda hatsarin ya ritsa da su. Ban taba ganin irin hakan ba. Daga abinda na ji wasu daga cikinsu shaye-shaye suka yi. Gayun da ke cikin Corolla din a buge suke.”

Daily Trust ta shaida yadda jami’an FRSC suke kwashe wadanda suka samu raunika zuwa asibiti tare da wadanda suka mutu zuwa ma’adanar gawawwaki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Sama Cike Da Fasinjoji Ya Yi Mummunan Hatsari, Mutane Da Yawa Sun Rasu

An ga jama’a masu tarin yawa da suka tsaya a wurin suna kallon mummunan hatsarin.

Matar aure ta bukaci a raba aurenta da mijinta kan duka da cin zarafi

A wani labari na daban, wata matar aure ta bayyana a gaban wata kotu da ke zama a Mapo a babban birnin tarayya na Abuja.

Ta bayyana yadda mijinta ya ke dukanta don boye kura-kuransa, cin zarafinta gabana jama'a da kin daukar dawainiyar gidansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng