Daga Siyan Zobo da Kunun Aya, Matashi Ya Yi Wuf da Mai Talla, Sun Zama Amarya da Ango

Daga Siyan Zobo da Kunun Aya, Matashi Ya Yi Wuf da Mai Talla, Sun Zama Amarya da Ango

  • Wata matashiya ‘yar asalin jihar Katsina ta samu rabo mai tsoka daga sana’ar siyar da Zobo da Kunun Aya a kafar Twitter
  • Ta yada labarin yadda ta auri wani kwastomanta yayin da a kwankwasa mata ‘DM’ don siyan abin da take siyarwa a kafar
  • Kafar Twitter na daya daga kafafen da ake kulla zumunta da alaka mai karfi, musamman aure a bangarori daban-daban na duniya

Jihar Katsina - Yayin da kafar sada zumunta ke iya zama kafar neman kudi ga wasu, bata lokaci ga wasu, takan iya zama silar cikar darajar mutum; ta hanyar samun miji ko mata don rayuwa.

Wata budurwa mai siyar da kayan makulashe da ababen sha a Twitter ta nunawa duniya alherin da ta samu a kafar yayin da ta sanar da aurenta da daya daga cikin kwastomominta.

Kara karanta wannan

Toh fa: Jami'a a Arewa ta haramtawa dalibai rike wayar hannu, jama'a sun yi martani

A cewar budurwar mai suna Aisha Sabi’u Bature, daga yi mata sallama don siyan Zobo da Kunun Aya, wani matashi mai suna Muhammad Sani Yawale ya yi wuf da ita.

Budurwa ta auri kwastoma daga siyan zobo da kunun
Daga Siyan Zobo da Kunun Aya, Matashi Ya Yi Wuf da Mai Talla, Sun Zama Amarya da Ango | Hoto: @ammahbaturee
Asali: Twitter

Maganarsu ta farko

A hotuna guda biyu da ta yada, Legit.ng Hausa ta ga rubutun da mutumin ya fara tura mata a Twitter, inda yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ta yaya zan samu Zobo da Kunun Aya masu sanyi ko ma dai mai kankara baki ajiye lambar waya ba don jin karin bayani daga dareki.”

Wannan batu dai shine mafarin zance a tsakaninsu, kuma tuni suka yi aure a ranar Asabar, 7 ga watan Janairun bana bayan da zance ya yi nisa, suka fahimci juna.

Martanin jama’a a Twitter

Yayin da mutan Twitter suka ga wannan batu, sun shiga mamaki tare da yi musu fatan alheri. Ga kadan daga martanin jama’a da muka tattaro muku:

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

@Bin__usup

“Allah na gani Ina San irin auren nan wlh ”

@Binkabir3

“Allah Ya bada zaman lafiya, nace ba sobo mai sanyi ya siya ko mara sanyi?”

@Jiddo_sadiq

“Da gaske ashe har anyi bikin ma na zaci watan Fabrairu ne fa. Allah ya sa alkhairi Allah ya baku zaman lafiya.”

@ahmed_shehu7

“Ni kaina daga Siyan Pizza ”

@nura_nuraddeen

"Kunun aya mai sanyi Allah sa albarka."

@BelloMB96

"Mutumina na ya samu sobo da Mai Sobo. Allah ya vada zaman lafiya."

@Hajjajo_

"Allah ya bada zaman lafiya.. Kamar dai sana'ar zobon nan zamu shiga "

Wani mutum na neman aure a Twitter, bazawara

Idan baku manta ba, a baya mun kawo muku labarin yadda wani mutum ke neman bazawara zai aura, kuma ya ba da cikiya ne a kafar Twitter.

Daga cikin abubuwan da yace zai ba matar da zai aura sun hada da sadakin N1m, kuma zai kara mata da N200,000.

Kara karanta wannan

Ba a Afrika kadai bane: Kamar dai na ASUU, malamai a Ingila za su shiga yajin aiki

Ya kuma bayyana cewa, bai bukatar ta zo da komai, domin kuwa ya riga ya shirya komai nasa a gida, kawai zuwan amarya yake jira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.