Ka Tausayawa Talakawan Karkara, Gwamnonin Najeriya Sun Bayyanawa Gwamnan CBN

Ka Tausayawa Talakawan Karkara, Gwamnonin Najeriya Sun Bayyanawa Gwamnan CBN

  • Ana saura kwanaki 10 karewar wa'adin da bankin CBN ya sa kan tsaffin Naira, gwamnonin Najeriya sun yi magana
  • Gwamnoni sun ce bankin CBN ya duba lamarin talakawan Najeriya kafin haramta amfani da tsaffin takardun Naira
  • Har yanzu akwai miliyoyin yan Najeriyan da ko ganin sabbin takardun N200, N500 da N1000 basu yi ba

Abuja - Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi kira ga babban bankin Najeriya da ya tausayawa talakawa da mutan karkara kafin daina amfani da tsohon kudi da kuma takaita adadin kuri'un za'a iya cirewa daga banki.

Wannan ya biyo bayan gayyatar da kungiyar gwamnonin ta yiwa gwamnan bankin, Godwin Emefiele, game da lamarin daina amfani da tsaffin kudin N200, N500, da N1000.

Saura kwanaki goma wa'adin da bankin ya sanya ya kare kan amfani da tsaffin kudin Naira.

Kara karanta wannan

Har Sambisa akwai sabbin kudi, mun tura ma'aikata wajen: Gwamnan CBN

New Naira
Ka Tausayawa Talakawan Karkara, Gwamnonin Najeriya Sun Bayyanawa Gwamnan CBN Hoto: Godwin Emefiele
Asali: UGC

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana hakan a jawabin da fitar ranar Alhamis bayan zaman kungiyar na farko a shekarar 2023, rahoton ChannelsTV.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa gwamnoni ba su adawa da lamarin sauya Naira amma fa akwai matsala.

Yace:

"Mu mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya mun samu jawabin Gwamnan babban bankin Najeriya, Mr Godwin Ifeanyi Emefiele, game da sauya fasalin Naira, tasirin da hakan ke da shi ga tattalin arziki da tsaro, har da dokar takaita adadin kudin da za'a iya cirewa."
"Gwamnonin ba su adawa da manufar sauya Naira. Amma mun fahimci cewa akwai kalubale da dama da suka addabi al'ummar Najeriya."

Saboda haka, Tambuwal ya bayyana cewa akwai bukatar CBN ta duba halin da jihohi ke ciki musamman lunguna da sakon da ko bankuna babu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wajibi Ne A Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Da Wata 6: Majalisar Dattawa Tayi Ittifaki

Sun yanke shawaran cewa:

"Zamu yi aiki da shugabannin CBN wajen tattaunawa da fashin baki game da wasu dokoki da suka shafi talakawa, marasa galihu da sauran yan Najeriyan da abin zai shafa."

CBN ya fadi kudaden da zai caji bankuna a kullum kan kin daukar sabbin Naira

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zargi ga bankunan yiwa gwamnatin zagon kasa game da lamarin sabbin kudaden Naira.

Bankin yace wasu bankuna da dama sun ki zuwa daukar sabbin kudin Naira da ya buga.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida