'Yan Najeriya Sun Shiga Mamaki Yayin da Jami’a a Arewa Ta Hana Dalibai Zuwa da Wayar Hannu
- Wata jami’a mai suna Bingham a jihar Nasarawa ta haramta amfani da wayoyin hannu saboda wasu dalilai
- Sanarwar da jami’ar ta fitar a kwanakin baya ta jijjiga intanet, mutane da yawa sun shiga mamakin hana daliban jami’a rike waya
- Mutane da yawa sun soki jami’ar da kokarin mai da rayuwar daliban ta koma baya ta hanyar mai dasu bayi
Jihar Nasarawa - Wata jami’a a jihar Nasarawa, Bingham University ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta bayan da ta fitar da wata sanarwa da ke haramta amfani da wayar salula ga dalibai a harabar makaranta.
A cewar wani hoto da aka yada a Instagram a ranar 20 ga watan Janairu a kafar @lindaikeblogoffocial, jami’ar mallakin cocin ECWA na addinin kirista.
Jami’ar ta fitar da wannan haramcin ne saboda samun matsala da ake yi a jami’ar na yadda dalibai ke amfani da wayar hannu ba tare da lissafi ba.
Sai kace makarantar sakandare
Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun shiga mamaki tare da caccakar makarantar bisa wannan haramci mai tsauri.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wasu da yawa sun nuna damuwar cewa, wannan doka ta yi kama da wacce ake sanyawa a makarantun sakandare a kasar.
Mutane da yawa sun tada tambayar cewa, wayoyin na da amfani wajen yin bincike ga daliban, ya kamata a duba lamarin.
Martanin jama’a
Ga abin da kadan daga mutanen soshiyal midiya ke cewa:
@okoye_ella_:
"Lmoa maraba da shiga jerin akalla ai daliban jami’ar Madonna sun dade suna rayuwa babu wayoyin hannu.”
@meekyfred:
“Wannan wane irin ci gaba da bautarwa ne ke faruwa nan?
@adangaijessica:
"Hukumar makarantar ya kamata su yi wani abu, dalibai 9 na kwana a dakin da aka yi don dalibai 4, ku kuba, kuma ana kara kudin makaranta.”
@omocatechist:
"Wannan ne yasa daliban makarantun kudi basu iya komai ba.”
@seun_dreams:
"Duk wadannan makarantun sakandare ne da ke kiran kansu jami’a.”
@thatguyosas:
"Aikin gida fa? Wadannan sun koma baya zuwa 1963.”
Dan Najeriya Ya Tarawa Wata Tsohuwa Tallafin Kudi a Kafar TikTok, Ya Kai Mata N1m Har Gida
A wani labarin kuma, wani dan Njeriya ya yi amfani da kafar TikTok wajen taimakawa wata mata da ke bukatar kudi.
Matashin ya sanarwa abokansa da ke bibiyarsa a TikTok cewa, su tara mata kudi, inda ya samar da Naira miliyan 1 gareta.
Mutane da yawa sun yi martani bayan ganin wannan lamari mai daukar hankali da ya faru da ya faru.
Asali: Legit.ng