Masarautar Katsina Ta Sake Tuɓe Rawanin Basarake Da Ke Haɗa Baki Da Ƴan Ta'adda
- Masarautar Katsina ta kori Makaman Katsina, hakimin Bakori, Idris Sule Idris, kan zarginsa da hannu a ta'addanci
- Korar da aka yi wa Idris Sule Idris na zuwa ne bayan kwamitin da gwamnatin jiha ta kafa don yin bincike ta same shi da laifi bayan mutanensa sun yi korafi
- A baya, gwamnatin na Katsina ta taba korar Sarkin Pawan Katsina, hakimin Kankara, Yusuf Lawal, shima kan alaka da ta'addanci
Jihar Katsina - Masarautar Katsina ta tabbatar da korar babban hakimi, Makaman Katsina, hakimin Bakori, Idris Sule Idris, kan zargin yana taimakawa da hannu a ta'addanci a yankinsa, rahoton Daily Trust.
Korar tasa na cikin wani wasika ne mai kwanan wata na 19 ga watan Janairun 2023, dauke da sa hannun Kauran Katsina, hakimin Rimi, Aminu Nuhu Abdulkadir, wanda mai nada sarki ne kuma babban mamba na masarautar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wasikar ta ce an kori Makama ne bayan kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa ta same shi da laifin aikata tuhume-tuhumen da mutanensa suka yi masa.
Wani sashi na wasikar ta ce:
"Biyo bayan wasikar da masarauta ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin jiha mai lamba da SEC/54/Vol. VI/1416, inda mai girma gwamna ya tabbatar da zargin da ake maka gaskiya ne.
"Zargin abin da aka maka sun janyo rashin zaman lafiya a yankin ka. Don haka, masarautar tana son sanar da kai cewa an sallame ka daga aikinka a matsayin Makaman Katsina, Hakimin Bakori."
Mai magana da yawun masarautar ya tabbatar da korar Makaman Katsina
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun masarautar Katsina, Ibrahim Bindawa ya tabbatar da korar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya ce:
"Eh, gaskiya ne."
Ba wannan bane karo na farko da aka korar masu sarautan gargajiya da ke ta alaka da yan ta'adda.
A shekarar 2021, masarautar Katsina ta kori Sarkin Pawan Katsina, hakimin Kankara, Yusuf Lawal, kan zarginsa da tallafawa yan ta'adda.
Kotun Kolin Najeriya Ta Tube Rawanin Basarake A Cross Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa kotun koli ta tube rawanin Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, mai sarautar Obong na Calabar.
A cewar Daily Trust, mai shari'a Mohammed Lawal Garba yayin yanke hukuncin ya umurci masu nada sarakuna su fara bin hanyar nada wani Obong na Calabar don maye gurbin Edidem.
Asali: Legit.ng