MOFI: Buhari Ya Dauko Tsohon Ministan ‘Yaradua, Ya ba Shi Mukami a Gwamnatinsa
- Gwamnatin tarayya ta yi nade-naden mukamai a ma’aikatar MOFI, an zabi sababbin shugabanni
- Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Dr. Shamsuddeen Usman ya jagoranci wannan babban aiki
- Ministar kasafin kudi tattalin arziki ta fitar da sunayen Darektocin da za su kula da MOFI a Najeriya
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya fara canza fasalin ma’aikatar tattalin arziki, yayin da ya nada wadanda za su kula da aikin MOFI a Najeriya.
This Day ta kawo rahoto cewa Muhammadu Buhari ya zabi Dr. Shamsudeen Usman a matsayin shugaban majalisar da za ta rika sa wa ma’aikatar ido.
Mai girma shugaban kasa ya nada Armstrong Katang a matsayin Babban Shugaban MOFI.
An fahimci wannan ne daga wani jawabi da ya fito daga bakin Mai taimakawa Ministar tattalin arziki wajen yada labarai, Yunusa Tanko Abdullahi.
Sanarwar Yunusa Tanko Abdullahi ta nuna an zabi mutane shida a majalisar da ke sa ido a ma’aikatar, sannan an nada mutane biyar a cikin shugabanni.
Darektoci marasa iko da aka nada a ma’ikatar tattalin arzikin sun hada da Sakatarorin din-din-din na ma’aikatun tattalin arziki da na man fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya bayyana cewa an dauko Akanta Janar na kasa da kuma wakilin babban bankin Najeriya da Barista Alheri Bulus Nyako sai Alhaji Muhammad Nda.
Vanguard ta ce sauran ‘yan majalisar sun hada da Olawale Edun, Hajiya Fatima Mede, Ike Chioke, Muhammad Nda da kuma Barrister Alheri Bulus Nyako.
Darektoci masu iko da za su rike MOFI su ne Sani Yakubu, Oluwafemi Owonubi da Eric Oji.
Wanene Dr. Shamsuddeen Usman
Usman wanda zai jagoranci aikin ma’aikatar ya rike kujerar Ministar tattalin arziki da tsare-tsaren kasafin Najeriya a lokacin mulkin Ummaru Musa ‘Yaradua.
MOFI na da alhalin kula da asusun wani jarin N30tr na musamman da kula da bashi.
Festus Keyamo SAN ya je kotu
An samu labari cewa Ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo SAN yana so a binciki Atiku Abubakar da karfi da yaji a wani dalilin bidiyo da aka fitar.
Ministan tarayyar ya bada wa’adin kwanaki uku domin a fara bincike, amma ba ayi komai ba, wannan ya jawo Keyamo SAN ya kai batun zuwa gaban kotu.
Asali: Legit.ng