Ba Na Son Daurawa Kowa Nauyi: Dalibi Mara Galihu Da Ke Bacci a Aji Ya Samu Taimako

Ba Na Son Daurawa Kowa Nauyi: Dalibi Mara Galihu Da Ke Bacci a Aji Ya Samu Taimako

  • Wani dalibi da ya mayar da ajin daukar karatunsu gidansa ya tsuma zukata a soshiyal midiya
  • Wani dan makarantarsu wanda ya gano matashin yana bacci ya ce ya lura cewa a nan yake kwanna kullun
  • Zamanin rashin galihunsa ya wuce, don haka ya je godiya ga abokin karatunsa wanda ya taimaka masa

Wani matashi wanda ke kwana a dakin daukar karatunsu bayan kammala darussa ya samu taimako daga dan makarantarsu.

Dan makarantar nasu ya wallafa bidiyon abokin karatun nasa da ba'a bayyana sunansa ba yana bacci kuma ya ce ya same shi a wajen sa'o'i uku bayan gama daukar darasi.

Matashi
Ba Na Son Daurawa Kowa Nauyi: Dalibi Mara Galihu Da Ke Bacci a Aji Ya Samu Taimako Hoto: TikTok/@mo2rawww
Asali: UGC

A cewar dan makarantar nasu, matashin na kwana ne a aji kullun. Dalibin mai matukar kirki ya tunkari abokin karatun nasa mara galihu sannan ya taimaka masa.

Dalibin mara galihu ya ki amsar taimakon, cewa baya so ya karawa kowa nauyi. Sai dai kuma ya yarda bayan an shawo kansa. Abokin karatun nasa mai kirki ya ce matashin na iya zama da shi na zangon karatun kasancewa abokin zamansa ya bar dakin.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kama Kifi Mai Launin Ruwan Gwal, Ya Nemi Sanin Darajarsa Kafin Ya Cinye, Bidiyon Yadu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya mallakawa matashin kwamfutar MacDonald sannan a karshen bidiyon ya sanar da cewar kawunsa zai biyawa dalibin kudin makarantarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Lykater Kimble222 ta ce:

“Hakan ya yi kyau. Allah ya yi maka da kawunka albarka. Ina rokon Allah ya sa wannan labarin ya bude idanun mutane da dama don su taimakawa mai bukatar taimako.”

Robert ya ce:

"Allah ya yi maka albarka yallabai, dukkanmu muna bukatar taimako lokaci zuwa lokaci, godiya gareka da ka taimakawa wannan matashin a tafiyarsa."

Risa Deane ta ce:

"Wannan ya sa ni kuka! Matashi na kokarin tallafawa wani! Wannan shine abun da muke bukatan zama ga junanmu. Hannun taimako, bangon jingina."

lizaquino1273 aka local ya ce:

"Kai mutumin kirki ne..kuma aboki na taya ka gode ma Allah., haka kuma kuma kawunka Allah ya albarkaceku dukka."

Kara karanta wannan

2023: Mutane Za Su Yi Alfahari da Kasancewarsu Yan Najeriya Idan Na Gaje Buhari, Peter Obi

Matashi mai tuka adaidaita sahu ya samu tallafi daga yan Najeriya

A wani labarin, wasu bayin Allah sun tallafawa wani matashi dan shekaru 16 da ke sana'ar adaidaita sahu da kudi N82,000 don ya koma makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng